‘Yan bindiga sun kai farmaki wani gari a Kaduna, sun jikkata mutum 12 tare da halaka daya

‘Yan bindiga sun kai farmaki wani gari a Kaduna, sun jikkata mutum 12 tare da halaka daya

  • 'Yan bindiga sun kai farmaki yankin Madaka da ke garin Kachia a karamar Hukumar Kachia da ke Jihar Kaduna
  • Mummunan lamarin wanda ya afku a daren ranar Laraba, ya yi sanadiyar rasa ran mutum daya tare da jikkata wasu 12
  • Rundunar yan sandan jihar ta tabbatar da lamarin, sai dai ta ce bata sani ba ko an yi garkuwa da wani

Mutum daya ya mutu yayin da wasu 12 suka samu raunuka a wani hari da ‘yan bindiga suka kai a yankin Madaka da ke garin Kachia a karamar Hukumar Kachia da ke Jihar Kaduna.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa mummunan al’amarin ya afku ne a ranar Laraba, 23 ga watan Yuni, da misalin karfe 11:00 na dare.

KU KARANTA KUMA: Da dumi-dumi: Sabon rikici ya kunno kai a PDP yayinda kotu ta tsige Shugaban jam’iyyar

‘Yan bindiga sun kai farmaki wani gari a Kaduna, sun jikkata mutum 12 tare da halaka daya
‘Yan bindiga sun jikkata mutum 12 tare da kashe daya a garin Madaka da ke Kaduna Hoto: nigeriantribuneng.com
Asali: UGC

Jaridar ta kuma ruwaito cewa wani jigon garin ya tabbatar da cewar an kashe mutum daya a harin.

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Kaduna ta tabbatar da harin, inda ta ce akalla mutane 12 ne suka samu raunuka kuma suna karbar magani a wani asibiti da ba a bayyana ba.

Jami'in Hulda da Jama'a na 'yan sanda, ASP Mohammed Jalige, ya ce ba zai iya tabbatar ko an sace wani ba.

Ya kara da cewa an shirya wata ganawa da kwamandan ‘yan sanda na yankin don samun cikakken bayani game da harin.

KU KARANTA KUMA: Rikicin Boko Haram: Wata Ƙasa Zata Ta Samar da Tallafin Dala Miliyan $26.95 Ga Yan Gudun Hijira

An Kwamushe Wani Sufeton ’Yan Sanda Dake Dillancin Makamai Da ’Yan Bindiga

A wani labarin kuma, wani Sufeton ‘yan sanda, Nathaniel Manasseh, ya shiga hannun 'yan sanda a Jihar Kuros Riba bisa zargin dillancin bindigogi da alburusai ga masu aikata laifuka.

An cafke Manasseh a Calabar, babban birnin jihar, kuma aka gabatar da shi a hedikwatar ‘yan sanda ranar Talata tare da sauran wadanda ake zargi da aikata miyagun laifuka, an ce shi babban dillalin bindiga ne kuma ya dade yana wannan harkallar kafin dubunsa ya cika.

Sufeton da ya amsa laifin shi, an ce shi ne ke kula da ma'ajiyar makamai a rundunar 'yan sanda ta jihar kuma an kama shi ne lokacin da ya kasa ba da bahasin wasu kayan aiki ciki har da bindigogin AK-47 guda biyu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel