Da dumi-dumi: Sabon rikici ya kunno kai a PDP yayinda kotu ta tsige Shugaban jam’iyyar

Da dumi-dumi: Sabon rikici ya kunno kai a PDP yayinda kotu ta tsige Shugaban jam’iyyar

  • Jam'iyyar PDP reshen jihar Legas ta wargaje bayan hukuncin kotu wacce ta kori shugabanta, Injiniya Deji Doherty
  • Babbar kotun jihar ta Legas ta kuma sake dawo da Dr Adegbola Dominic a matsayin shugaban jam'iyyar adawa ta Legas
  • Yayin da Dominic ya ce zai ci gaba da bin hukuncin kotun, Doherty ya bugi kirjin cewa hukuncin ba zai yi tasiri ba, cewa za a daukaka kara

Babbar kotun jihar Lagas ta kori da Injiniya Babbar Deji Doherty, shugaban jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) reshen jihar.

Kotun ta kuma sake dawo da Dr Adegbola Dominic a matsayin shugaban jam’iyyar adawa a Legas, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Da dumi-dumi: PDP ta dakatar da shahararren dan majalisa kwanaki 4 bayan kayar da EFCC a kotu

Da dumi-dumi: Sabon rikici ya kunno kai a PDP yayinda kotu ta tsige Shugaban jam’iyyar
Akwai wani sabon rikici a jam'iyyar PDP reshen jihar Legas biyo bayan hukuncin kotu da ta kori shugaban jihar, Engr. Deji Doherty Hoton: Adedeji Doherty
Asali: Facebook

Legit.ng ta tattaro cewa kotun ta amince da hujjar Dominic wanda ya kai PDP kotu cewa babu wani gurbi a jam'iyyar.

Dominic ya kalubalanci babban taron jam'iyyar na musamman da aka gudanar a watan Nuwamba na 2019, yana mai cewa har yanzu shi ne shugabanta na ainahi tunda ya maye gurbin tsohon shugaban da ya yi murabus daga jam'iyyar, jaridar Nigerian Tribune ta kuma ruwaito.

Da yake yanke hukuncin, Mai Shari’a Oyekan Abdullahi ya riki korafin farko da wadanda ake karar suka gabatar cewa bai da tasiri sannan kuma yayi watsi da su.

KU KARANTA KUMA: Buhari, Gwamnonin Arewa sun sa labule a Aso Villa a kan matsalar rashin tsaro

Abdullahi ya yanke hukuncin cewa an nada Dominic ne bisa cancanta don kare wa’adin magabacin nasa wanda ya yi murabus.

Dominic ya shirya dauka daga inda aka tsaya

Da yake magana da Daily Trust, Dominic a ranar Laraba, 23 ga Yuni, ya ce a shirye yake ya ci gaba da tafiyar da harkokin jam’iyyar nan take.

Ya kara da cewa hukuncin ya bayyana karara cewa babu wani gurbi a jam'iyyar tun farko.

Dominic ya kuma ce yana tattaunawa da hukumomin tsaro da niyyar hanzarta ci gaba da kasancewarsa a matsayin shugaban jihar kafin ranar Juma'a, 25 ga watan Yuni.

Doherty yayi martani game da hukuncin

Sai dai kuma, Doherty ya bayyana cewa hukuncin da ya sake dawo da Dominic a matsayin shugaban jam’iyyar a jihar ba shi da wani cancanta don haka ba zai yi tasiri ba.

Ya bayyana cewa jam'iyyar na da wa'adin kwanaki 14 don daukaka kara kan hukuncin, yana mai cewa shine shugaban jam'iyyar kuma ya kammala taron kwamitin aiki na jihar.

Doherty ya kara da cewa sakatariyar jam'iyyar ta PDP ta kasa za ta yi nazari kan hukuncin idan aka gabatar mata da shi kuma za ta yi abin da ya dace.

Ya ce Dominic ba shi da abin da zai karbi mulki tunda shugabannin jam’iyyar PDP na kasa ba su amince da shi a matsayin shugaban jihar Legas ba.

A wani labarin, wani dan majalisar dokokin jihar Nasarawa mai wakiltar Mazabar Karu / Gitata a karkashin inuwar jam’iyyar PDP, Maiyaki David ya sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki a jihar.

Kakakin majalisar, Ibrahim Balarabe Abdullahi wanda ya karanta wasikar ficewar dan majalisar ya ce Maiyaki ya bar tsohuwar jam’iyyarsa zuwa APC ne saboda amfanin jama’arsa, jaridar The Nation ta ruwaito.

Kamar yadda yake a yanzu, APC na da mambobi 20; PDP tana da mambobi uku sai kuma Zenith Labour Party (ZLP) dake da daya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng