Wani mutum ya damke Abokinsa na kut-da-kut tsirara a gidansa, ya na neman Mai dakinsa

Wani mutum ya damke Abokinsa na kut-da-kut tsirara a gidansa, ya na neman Mai dakinsa

  • Wani Bawan Allah ya kama Amininsa ya shigo masa gida zai yi lalata da matarsa
  • An kama wannan mutumi tunbur bayan matar da mijinta sun shirya masa tarko
  • Da wannan kwarto ya fara neman matar auren, sai ta yi maza ta sanar da mijinta

Rahotanni daga jaridar Katsina Post sun bayyana cewa wani mutumi ya cafke abokinsa tunbur haihuwar uwarsa, ya shiga gidansa ya na neman matarsa ta aure.

Kamar yadda muka samu labari, wannan Bawan Allah ya yi ram da amininsa a gidansa, ya je kwartanci, wannan lamari ya auku a unguwar Modoji, jihar Katsina.

Jaridar ta ce ta sakaya bayanan da suka shafi wadannan mutane domin a tsare masu mutuncinsu.

KU KARANTA: Mai gida ya dawo, kwarto ya diro ta 'taga' daga gidan sama

Wadanda abin ya auku a gaban idansu, sun tabbatar wa manema labarai cewa mutumin da aka kama dumu-dumu a gidan matar aure, aminin mijin wannan mata ne.

An cafke wannan mutum tsirara ya je kwartancin a ranar Lahadi, 19 ga watan Yuni, 2021, da yamma.

Ya dade ya na neman damar yin lalata

Majiyar ta ce wannan kwarto ya dauki tsawon lokaci ya na neman maidakin amininsa, amma bai samu goyon bayan yin danyen aikin ba, kuma har ta fada wa mijin na ta

Rahoton ya ce shi kuwa mijin bai yarda da maganar ba a lokacin da aka fara bijiro masa da ita, ganin irin dangatakar da ke tsakaninsa da wannan babban abokin na sa.

KU KARANTA: Motar mai ta kife, ta jawo gobara a titin Legas zuwa Ibadan

Ga abin da wani wanda ya san abin da ya wakana ya ce: “Matar ta dade tana fadawa mijin nata cewar abokin sa yana yi mata maganganun banza har ma yana neman ta.

“Amma shi mijin ya musanta kalaman matar saboda kallon irin alakar abokantar da ke tsakanin su.”

Dubu ta cika

Ranar da za a cafke shi, sai aka yi masa tarko, mai gidan ya boye a rufin kwanon gida, kwarton ya lallabo, har ya tube kaya, sai aka damke shi, yanzu ya na hannun ‘yan sanda.

A bara kun ji labarin wani dan kasuwa a Ibadan, Abdullateef Babatunde, da ya fada wa kotu cewa sau biyu kwarto ya na yi wa matarsa ciki, amma ya hakura, ya kauda kansa.

Mutumin yake cewa matarsa ta kasance mai cin amanar sa a aure, ya sha cafke ta da mazan banza.

Asali: Legit.ng

Online view pixel