Rikicin Boko Haram: Wata Ƙasa Zata Samar da Tallafin Dala Miliyan $26.95 Ga Yan Gudun Hijira
- Ƙasar Canada ta sanar da shirin samar da kuɗi kimanin dala miliyan $26.95 domin tallafawa mutanen yankin arewa-gabas
- Wannan na ƙunshe ne a cikin wani jawabi da ofishin jakadancin ƙasar a Najeriya ya fitar ranar Laraba da yamma
- Ƙasar tace rikicin da ya addabi yankin arewa-gabas a Najeriya yana daga cikin mafi girma a duniya
Gwamnatin Canada ta sanar da samar da tallafin kuɗi dala miliyan $26.95 domin taimaka wa al'ummar da rikicin Boko Haram ya shafa a yankin arewa maso gabas, kamar yadda premium times ta ruwaito.
KARANTA ANAN: Dalilin da Yasa Muke Maida Yan Gudun Hijira Gudajensu Duk da Akwai Ƙalubalen Tsaro, Zulum
Gwamnatin Canada ce ta sanar da haka a wani jawabi da ta fitar ta ofishin jakadancinta dake Najeriya ranar Laraba da yamma.
Wani sashin jawabin yace:
"Waɗannan kuɗaɗen zasu taimaka wajen samar da tallafin abinci, kula da lafiya, samar da tsaftataccen ruwa da sauran kayan kariya."
"Rikicin da ya dabai-baye yankin arewa-gabas a Najeriya na tsawon shekaru ya shiga sahun rikice-rikice mafiya girma a duniya, inda ake ƙiyasin akwai mutum aƙalla miliyan 8.7m dake buƙatar taimakon don gudanar da rayuwarsu."
"Sannan akwai aƙalla mutum miliyan 4.4m da ake tsammanin suna matsanancin buƙatar taimakon abinci."
KARANTA ANAN: Ganduje: Aikin Ta'addanci a Najeriya Ya Shiga Mataki Na Gaba 'Next Level'
A kwanan nan ne, gwamna Babagana Umaru Zulum na jihar Borno, yace gwamnatinsa na maida yan gudun hijira gidajensu ne domin su noma gonakinsu.
Gwamnan yace yan gudun hijira aƙalla 10,000 daga Damasak, waɗanda suka bar ƙauyukan noman su a jihar Borno, yanzun sun koma gidajen su, kamar yadda premium times ta ruwaito.
A wani labarin kuma Wani Fitaccen Malami Yace Haramun Ne Yin Amfani da Alamar Dariya a Facebook
Wani fitaccen malamin addinin musulunci yace haramun ne amfani da alamar dariya a facebook domin muzgunawa wani.
Malamin mai amfani da suna ɗaya, Ahmadullah, yana da tarin mabiya a kafafen sada zumunta.
Asali: Legit.ng