Jam’iyyar PDP ta yi babban rashi na dan majalisarta a Nasarawa, ya sauya sheka zuwa APC

Jam’iyyar PDP ta yi babban rashi na dan majalisarta a Nasarawa, ya sauya sheka zuwa APC

  • Dan majalisar dokokin jihar Nasarawa mai wakiltar Mazabar Karu / Gitata Maiyaki David ya sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa APC
  • Maiyaki ya bayyana cewa ya yanke wannan shawara ne domin ra'ayin mutanen da yake wakilta
  • A yanzu APC na da mambobi 20 a majalisar dokokin jihar Nasarawa, PDP na da uku yayinda ZLP ke da daya

Wani dan majalisar dokokin jihar Nasarawa mai wakiltar Mazabar Karu / Gitata a karkashin inuwar jam’iyyar PDP, Maiyaki David ya sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki a jihar.

Kakakin majalisar, Ibrahim Balarabe Abdullahi wanda ya karanta wasikar ficewar dan majalisar ya ce Maiyaki ya bar tsohuwar jam’iyyarsa zuwa APC ne saboda amfanin jama’arsa, jaridar The Nation ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Biloniya kike aure: An yi cece-kuce yayin da Zahra Buhari ta ce aure na nufin soyayya mara iyaka a gare ta

Jam’iyyar PDP ta yi babban rashi na dan majalisarta a Nasarawa, ya sauya sheka zuwa APC
David Maiyaki ya sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa APC Hoto: The Nation
Asali: UGC
“Da sauya shekar David Maiyaki, yanzu haka muna da mambobin Majalisar guda 10 daga shiyyar, dukkansu suna cikin APC. Kofofinmu a bude suke kuma har yanzu ina sa ran sauran mambobi hudu su dawo cikinmu nan ba da dadewa ba,” in ji Kakakin.

Kamar yadda yake a yanzu, APC na da mambobi 20; PDP tana da mambobi uku sai kuma Zenith Labour Party (ZLP) dake da daya.

David Maiyaki ya ce ya yanke shawarar komawa APC ne domin amfanin mutanen mazabarsa da ma jihar baki daya, jaridar Sun ta ruwaito.

Maiyaki, wanda shi ne Shugaban Kwamitin Majalisar Dokoki kan filaye da bincike ya ce ya tuntubi mutanensa kan shawarar da ya yanke na barin PDP zuwa APC.

KU KARANTA KUMA: Zaben maye gurbi: APC ta lallasa PDP a mazabar Gwaram ta tarayya dake Jigawa

Zaben maye gurbi: APC ta lallasa PDP a mazabar Gwaram ta tarayya dake Jigawa

A wani labarin, mun ji cewa Alhaji Yusuf Galami, dan takarar jam'iyyar APC a zaben maye gurbi da aka yi domin cike kujerar majalisar tarayya ta mazabar Gwaram a jihar Jigawa ya samu nasara.

Farfesa Ahmad Shehu, baturen zaben, bayan tattara kuri'u daga akwatuna 248 ya bayyana Galambi a matsayin mai rinjaye da kuri'a 29,372 a kan Kamilu Inuwa na jam'iyyar PDP da ya samu kuri'u 10,047.

"Bayan Galambi ya samu kuri'u mafi rinjaye a zaben maye gurbin, ya zama mai nasarar a zaben," Shehu ya sanar da hakan a ranar Lahadi a Gwaram kamar yadda jaridar The Guardian ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel