Da dumi-dumi: PDP ta dakatar da shahararren dan majalisa kwanaki 4 bayan kayar da EFCC a kotu

Da dumi-dumi: PDP ta dakatar da shahararren dan majalisa kwanaki 4 bayan kayar da EFCC a kotu

  • Kwamitin aiki na jam'iyyar PDP a jihar Delta ya dakatar da Sanata Peter Nwaoboshi
  • Sakataren yada labarai na PDP a jihar, Dr. Ifeanyi M. Osuoza ne ya sanar da dakatar da Nwaoboshi a ranar Laraba, 23 ga watan Yuni
  • Dan majalisar da ke wakiltar Delta ta Arewa a majalisar dattawa har yanzu bai mayar da martani kan dakatarwar ba

Biyo bayan zarge-zargen da ake yi masa na ayyukan da suka saba jam’iyya, reshen jihar Delta na jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP) ta dakatar da Sanata Peter Nwaoboshi.

Jaridar Nigerian Tribune ta ruwaito cewa an dakatar da dan majalisar mai wakiltar Delta ta Arewa na tsawon wata daya a ranar Laraba, 23 ga watan Yuni.

KU KARANTA KUMA: Yadda 'yan bindiga ke samun makamai daga jami'an tsaro, Sheikh Gumi ya yi zargi mai karfi

Da dumi-dumi: PDP ta dakatar da shahararren dan majalisa kwanaki 4 bayan kayar da EFCC a kotu
Jam'iyyar PDP ta dakatar da Sanata Peter Nwaoboshi Hoto: Nigerian Tribune

Sakataren yada labarai na jam’iyyar PDP a jihar, Dr. Ifeanyi M. Osuoza wanda ya sanar da dakatarwar ya ce an yanke hukuncin ne a taron gaggawa na Kwamitin Aiki na jam’iyyar a jihar.

Ya ce:

“Wannan matakin ya zama dole a kan soyayyar da yake nunawa wata Jam’iyyar adawa, yin kalaman ganganci, da kalaman da ba su dace ba na Sanata Peter Nwaoboshi, musamman ga mutum kamar Mai Girma, Sanata Dr Ifeanyi Okowa, Gwamnan Jihar Delta, wanda Kwamitin Aiki na PDP a jihar yake kallon abin a matsayin ba mai karbuwa ba, mai tayar da hankali da rashin dacewa daga dan siyasa kuma dan jam’iyya mai kima.”

KU KARANTA KUMA: Gumi: Makiyaya suna satar yara ne kawai don kudi, sun fi yan IPOB

Sanata Nwaoboshi ya kayar da EFCC a kotu

Lamarin na zuwa ne 'yan kwanaki bayan wata babbar kotun tarayya da ke jihar Lagas ta sallami tare da wanke dan majalisar.

Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ta zargi Nwaoboshi da yin sama da fadi da Naira miliyan 322.

Da yake karanta hukuncin, Mai Shari’a Chukwujekwu Aneke ya ce hukumar ba ta tabbatar da hujjoji na laifukan da ta tuhumi Nwaoboshi ba, ya kara da cewa ba a kira shaidu don bayar da shaida ba, jaridar The Nation ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel