Buhari, Gwamnonin Arewa sun sa labule a Aso Villa a kan matsalar rashin tsaro

Buhari, Gwamnonin Arewa sun sa labule a Aso Villa a kan matsalar rashin tsaro

  • Gwamnonin yankin Arewa sun zauna da Shugaba Muhammadu Buhari a Aso Villa
  • Makasudin taron shi ne yadda za a shawo kan matsalar tsaro, a samu zaman lafiya
  • Gwamnatin Tarayya ta na so ayi maganin matsalar tsaro don mutane su koma gona

Mun samu labari cewa Shugaba Muhammadu Buhari, ya zauna da gwamnonin jihohin Arewa a fadar Aso Villa a ranar Laraba, 23 ga watan Yuni, 2021.

Kamar yadda rahotanni suka tabbatar, an yi wannan zama ne duba da halin tsaro da yankin Arewacin Najeriya yake fuskanta a daidai wannan marra.

Rashin tsaro a jihohin Arewa

This Day ta ce an tattauna game da abin da ya shafi tsaron jihohi 19 na yankin Arewa a wannan zama da aka yi ba tare da ‘yan jarida sun samu halarta ba.

KU KARANTA: Amotekun ta fadi abin da yake kawo mata cikas wajen kama Miyagu

Wasu gwamnonin yankin sun samu halartar wannan zama, daga ciki akwai gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle da Abubakar Sani Bello na Neja.

Legit.ng Hausa ba ta samu cikakken labarin wadanda aka yi wannan muhimmin taro da su ba.

An yi wannan gana wa da wasu gwamnonin ne bayan kammala taron majalisar zartarwa ta FEC wanda aka saba yi duk ranar Laraba a fadar shugaban kasa.

Wannan zama shi ne na biyu da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi da gwamnonin na Arewa a cikin watanni biyu, ya hadu da su a karshen Afrilu.

Wasu Gwamnonin Arewa
Gwamnonin Arewa a fadar Shugaban kasa Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Mai neman takarar Gwamna ya yi karar INEC da Shugaban PDP a Kotu

Jaridar Tribune ta tabbatar da cewa Mai girma gwamna Bello Matawalle ya yi magana bayan taron, inda ya shaida wa manema labarai wainar da aka toya.

Ruwa ya sauko, damina ta zo

“Na yi masa (Buhari) jawabi, gwamnan Neja ma ya yi masa bayanin halin da ake ciki. Shugaban kasa ya yi alkawarin zai dauki mataki kan batun rashin tsaro.”

Matawalle a madadin sauran abokin aikinsa ya ce manoma za su iya koma wa gona, su yi shuka, a cewarsa an samu zaman lafiya a watanni hudun bayan nan.

A jiya ne rahoto ya zo maku cewa jami’an tsaro suna cigaba da damke masu taimaka wa ‘Yan ta’addan Boko Haram inda aka yi ram da wani Wida Kachalla.

Wida Kachalla wanda yake tare da Modu Sulum, ya hadiye SIM dinsa da ya gane Sojoji sun rige sun rutsa shi a wata babbar kasuwa da ke garin Maiduguri, Borno.

Asali: Legit.ng

Online view pixel