Matawalle ya gana da Buhari, ya fadi yadda arewa ke farfadowa daga rashin tsaro
- Gwamman jihar Zamfara, Matawalle ya bayyana halin da arewa ke ciki a yanzu
- Gwamnan ya ce duk da tabarbarewar tsaro, amma yankin na farfadowa ahankali
- Ya kuma bayyana cewa, gwamnati ta tsara yadda manoma zasu koma gonakinsu
Bello Matawalle, gwamnan jihar Zamfara, ya ce sannu a hankali yankin arewa na fuskantar ci gaba a fannin tsaro, The Cable ta ruwaito.
Matawalle ya bayyana hakan ne a ranar Laraba lokacin da yake zantawa da manema labarai na gidan gwamnati bayan ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Gwamnan na Zamfara ya kasance a Abuja tare da Sani Bello, takwaransa na jihar Neja da kuma gwamnan jihar Kebbi, Alhaji Abubakar Atiku Bagudu, The Punch ta tattaro.
KU KARANTA: Duk wanda bai nuna shaidar ya yi NYSC ba kada a dauke shi aiki, DG ya ja kunne
A cewar Matawalle, duk da karuwar matsalolin kalubalen tsaro a kwanan nan, sabuwar hanyar da gwamnatin tarayya da jiha suka amince da ita tana samar da kyakkyawan sakamako.
Ya kara da cewa gwamnati za ta tabbatar da cewa an karfafa tsaro domin baiwa manoma damar komawa gonakinsu don noma da dasa shukokinsu a lokacin damina.
A cewar Matawalle:
“A cikin watanni hudu da suka gabata, ba mu fuskanci yawaitar samun rikici ba, amma sannu a hankali yana dawowa. Amma hukumomin tsaro suna iyakar kokarinsu a yanzu, musamman daga sabon tsarin tsaro da muka tsara yanzu. Muna samun ci gaba a kan kalubalen.
“Tare da aiki da kuma mafitar da muka zana tsakanin gwamnati da tsaro, muna yin iya kokarinmu don ganin cewa manoma sun koma gonakinsu kuma sun iya yin noma, insha Allah. Zamuyi iya kokarin mu don ganin cewa duk manoma sun koma gonakin su."
Matawalle ya kuma kara da cewa shugaban kasar ya basu tabbacin za a dauki mataki kan batutuwan da aka tattauna game da rashin tsaro.
KU KARANTA: Cikakken Bayani: Da Ma Ginin Majalisar Dokoki ta Kasa Na Bukatar Gyara, Lawan
Sojoji sun karyata Sheikh Gumi kan cewa jami'ansu na hada baki da 'yan bindiga
A wani labarin daban, Rundunar Sojin Najeriya ta karyata zargin Sheikh Ahmad Gumi na cewa jami’anta suna hada baki da ‘yan bindiga wadanda suka kasance masu aikata laifuka daban-daban da cin zarafin da ake yi wa 'yan Najeriya.
Daraktan, Hulda da Jama’a na rundunar, Onyema Nwachukwu, a cikin wata sanarwa a ranar Laraba, ya mai da martani ga zargin da Gumi ya yi a shirin ARISE TV Morning Show a ranar Laraba, Daily Trust ta tattaro.
Mista Nwachukwu ya ce sojojin Najeriya sun kasance wata alama ta hadin kan kasa mai sauke nauyin da kundin tsarin mulki ya dora mata bisa mafi kwarewar aiki daidai da tsarin duniya.
Asali: Legit.ng