Cikakken Bayani: Da Ma Ginin Majalisar Dokoki ta Kasa Na Bukatar Gyara, Lawan

Cikakken Bayani: Da Ma Ginin Majalisar Dokoki ta Kasa Na Bukatar Gyara, Lawan

  • Biyo bayan cece-kuce da aka dinga yi game da ambaliyar ruwan da ya faru a majalisar, Lawan ya yi bayani
  • Ya bayyana cewa, dama tun tuni majalisar na bukatar gyara, wanda har lokaci ya wuce ba a yi ba
  • Hakazalika majalisar ta dattawa ta koka kan karairayin da aka ruwaito game da abinda ya faru a majalisar

Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan a ranar Laraba ya ce ginin Majalisar Tarayya ya wuce lokacin gyarawa a halin yanzu, ya kara da cewa kwararar ruwa da ambaliyar sun tabbatar da matsayin shugabancinsa na neman a gyara ginin, The Nation ta ruwaito.

Lawan ya yi magana ne biyo bayan wani umarni da Mataimakin Shugaban Marakin Majalisar Dattawa, Sanata Aliyu Sabi Abdullahi ya gabatar yayin zaman majalisar, kamar yadda ya bayyana a shafin Facebook na majalisar.

Abdullahi ya yi korafin cewa, wasu rahotannin da kafafen yada labarai ke yadawa game da malala da ambaliyar ruwa da ya faru a dakunan majalisar saboda mamakon ruwan sama a ranar Talata, suna cike da rashin gaskiya, don haka ya zargi mutuncin 'yan majalisar.

KU KARANTA: Duk da tsawon tarihin Gurasa a Kano, 'yan Gurasa sun yi barazanar daina sana'ar

Da dumi-dumi: Ginin Majalisar Dokoki ta Kasa ya wuce lokacin gyara, in ji Lawan
Ambaliyar ruwa a majalisar dattawan Najeriya | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Yayin da yake bayyana umarni na 14 da 15 na Dogaro na Dattawan, Abdullahi ya ce:

“Batun ruwan sama mai nauyi kamar yadda ya faru a ranar Talata, kafafen watsa labarai daban-daban sun ruwaito shi.
"Ko da yake lokacin da na saurari rahoton a gidan Talabijin na Channels, akwai batutuwa da yawa da suka taso a cikin rahoton na su wanda na ji ya shafi mutunci na kuma hakika, da mutuncin abokan aiki na.
“A wancan rahoton, an ruwaito abubuwa uku wadanda ba gaskiya bane. Cewa anyi ruwan sama mai karfi kuma ya malala a dakin majalisa saboda yoyo. Hakan ba gaskiya bane.
"Tabbas an yi ambaliyar ruwa a kusa da harabar da ke wajen dakin majalisa. Hakanan an ruwaito cewa saboda wannan ambaliya an jinkirta zaman mu. Hakan ma ba gaskiya bane.

A cikin jawabinsa, Shugaban Majalisar Dattawan ya ce ambaliyar da aka yi a farfajiyar Majalisar Tarayya da aka gani ranar Talata, ya tabbatar da kokarin da shugabannin ke yi na ganin an gyara ginin.

Lawan ya ce:

“Bari na kuma ce mai yiwuwa mai rahoton gidan talabijin na Channels TV ba shi ne ke da alhakin wannan rahoton ba, mambobinmu na kungiyar 'yan jaridu suna sane da abin da muke yi a nan da kuma abin da ke faruwa a kusa da mu.
“Bari in ba 'yan jarida shawara, wannan ba daidai bane. Dole ne in ce, ku nemi gaskiya, ku yi bincike yadda ya kamata kafin ku tattara ku aika rahoton ku.
“Gaskiyar cewa akwai yoyo daga sama a wurina shaida ce karara, tabbatarwa da kuma nuni da matsayin da Majalisar Kasar ta dauka da farko.
“Kowa ya san cewa wannan wurin ya kai lokacin da ya dace a gyarashi. Mun je ganin Shugaban kasa kuma ya yi mana alheri kuma ya ce mu hadu da FCTA, masu ginin.
“Ni kaina, Shugaban Majalisa, marigayi Shugaban Ma’aikata da Ministan Kudi mun hadu don neman kudi saboda a gyara Majalisar Dokoki ta Kasa.
“Lokacin da aka amince da N37bn ba kasafin majalisar kasa ba ne, kasafin na FCDA ne.
“Muna sa ran manema labarai za su sanar da mutane yadda lamarin yake.
“Wannan gidan na 'yan Najeriya ne. Na ‘yan Najeriya ne kuma ya cancanci a gyara shi.”

KU KARANTA: Wani Kwamishina Ya Rigamu Gidan Gaskiya, Gwamna Ya Bayyana Ranar Hutu Saboda Jimami

Majalisa za ta binciki gwamnatin Buhari kan shirin farfado da tattalin arziki

A wani labarin, Majalisar dattijai a ranar Talata ta tambayi kwamitocinta a kan Tsarin Kasa; Banki, Inshora da sauran Cibiyoyin Kudi.

Ciki har da na Sufurin Ruwa; Sufurin Kasa da Ayyuka da Wuta don tattaunawa tare da Ministar Kudi, Kasafin Kudi da Tsare-Tsaren Kasa, Zainab Ahmed, kan shirin Farfado da Tattalin Arzikin Gwamnatin Tarayya na 2017 zuwa 2020, Daily Trust ta ruwaito.

Wannan ya biyo bayan wani yunkuri ne "kan bukatar tantance tasiri kan ayyukan Tattalin Arziki da Ci Gaban Kasa (ERGP) na 2017 zuwa 2020" wanda Sanata Abdu Suleiman Kwari ya dauki gabatarwa majalisa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.