'Barayi sunyi hatsari cikin motar da suka sace, ɗaya ya mutu biyu sun jikkata

'Barayi sunyi hatsari cikin motar da suka sace, ɗaya ya mutu biyu sun jikkata

  • Wasu da ake zargin yan fashi da makami ne sunyi hatsari bayan sace motar wani bawan Allah a Ondo
  • Wanda aka sace wa motar ya iso asibitin inda ya tarar da yan sanda sannan ya bada bayanin yadda suka masa fashin
  • Kwamishinan yan sanda ya bada umurnin a tisa keyarsu zuwa sashin binciken manyan laifuka CIID da zarar asibiti ta sallame su

Wasu mutum uku da ake zargin yan fashi da makami ne, sun yi hatsarin mota a ranar Asabar a Ode-Remo, jihar Ogun yayin da suke kokarin tserewa da motar da suka yi fashinta da bindiga, Premium Times ta ruwaito.

Daily Trust ta ruwaito cewa mai magana da yawun yan sandan jihar Ogun, Abimbola Oyeyemi ne ya sanar da hakan a ranar Laraba.

Wadanda ake zargi da fashin mota
Wadanda ake zargi da fashin mota. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Wasu Fulani 10 ƴan gida ɗaya sun mutu bayan sun kwankwaɗar wani maganin gargajiya

Mr Oyeyemi ya ce suna tserewa ne cikin wata mota kirar Toyota Camry da suka karbe a hannun wani da bindiga a jihar Ondo.

Daya daga cikin wadanda ake zargin ya mutu yayin da ake masa magani a asibiti a cewar yan sandan.

A cewar Oyeyemi, wadanda ake zargin suna asibiti ana musu magani sai DPO na Ode Remo, Fasogbon Olayemi ya samu rahoto cewa motar da aka yi hatsarin da ita na sata ne.

DUBA WANNAN: Da Duminsa: Allah ya yi wa jigo a jam'iyyar APC rasuwa a Zamfara

Matakin da yan sanda ta dauka kan wadanda ake zargin

Ya ce nan take DPO ya ce a tsare su a asibitin.

"Mai motar ya taho tun daga jihar Ondo ya yi bayanin cewa wasu gungun mutane biyar sanye da kaya irin ta yan sanda da bindigu ne suka tare shi suka kwace motarsa da karfi da yaji suka tafi," in ji shi.

Kwamishinan yan sanda, Edward Ajogun, nan take ya bada umurnin a tura sauran mutanen biyun da ake zargi, Sunday Emmanuel da Idris Ibrahim zuwa sashin binciken manyan laifuka, CIID, don zurfafa bincike.

A wani labarin daban, kun ji cewa Gwamna Bello Muhammad Matawalle na jihar Zamfara ya bukaci mazauna jiharsa su kare kansu daga hare-haren yan bindiga kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Daily Trust ta ruwaito cewa ya yi wannan furucin ne yayin wata addu'a ta musamman da aka shirya domin cikarsa shekaru biyu kan mulki.

Ya ce ya zama dole a samu zaratan jaruman matasa da za a daura wa nauyin dakile bata garin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel