Yadda 'yan bindiga ke samun makamai daga jami'an tsaro, Sheikh Gumi ya yi zargi mai karfi

Yadda 'yan bindiga ke samun makamai daga jami'an tsaro, Sheikh Gumi ya yi zargi mai karfi

  • Shahararren malamin addinin Islama, Sheikh Ahmad Gumi, ya ce hukumomin tsaro suna da tambayoyin da za su amsa game da ayyukan 'yan fashi
  • Gumi ya nuna damuwa game da yadda 'yan fashin ke samun makaman da suke amfani da su wajen aikata satar mutane da sauran laifuka
  • Shehin malamin ya bukaci gwamnatin tarayya da ta tattauna da makiyaya da 'yan bindiga don sanin matsalolin da ke haifar da tashin hankalinsu

Shahararren malamin addinin Islama, Sheikh Ahmad Gumi, ya yi zargin cewa akwai hadin baki tsakanin 'yan fashi da jami'an tsaro.

Jaridar The Cable ta ruwaito cewa Gumi yayi wannan zargin ne a ranar Laraba, 23 ga watan Yuni, yayin wata hira da shi a gidan talabijin na Arise TV.

KU KARANTA KUMA: Zargin zambar N7.1bn: Kotun Abuja ta sanar da ranar da za a sake gurfanar da tsohon gwamnan, Orji Uzor Kalu

Yadda 'yan bindiga ke samun makamai daga jami'an tsaro, Sheikh Gumi ya yi zargi mai karfi
Sheikh Gumi ya zargi wasu daga cikin jami'an tsaro da hada kai da 'yan bindiga Hoto: Dr. Abubakar Gumi.
Asali: Facebook

Gumi ya yi ikirarin cewa 'yan fashi suna samun makaman da jami'an tsaro ke rike da su

Ya yi ikirarin cewa hukumomin tsaro na ba 'yan ta'adda damar mallakar tarin kayan makamai da suke rike da shi.

Malamin ya ce, yanzu haka 'yan bindigar sun dauki satar mutane a matsayin kasuwanci.

Ya ce:

“Waɗannan’ yan fashi, idan ba ku sani ba, suna haɗa kai da yawancin bara gurbi a cikin tsarin tsaronmu. Wannan kasuwanci ne. Mutane da yawa suna da hannu, za ku yi mamaki sosai.”

Gumi ya yi tambaya kan yadda makaman da 'yan fashi ke amfani da su ke bi ta kan iyakokin zuwa daji.

KU KARANTA KUMA: Najeriya za ta ci gaba da zama kasa daya da ba za ta rabe ba, Ganduje

Ya ce:

“An kama su a Zamfara; an kama su a ko'ina, ta yaya waɗannan manyan makamai suke ketare iyakokinmu? Ta yaya wadannan manyan makamai zasu iya ketara iyakokin mu su shiga daji ba tare da hadin kan wasu miyagun jami'an tsaro da ke taimaka masu ba? Ba zai yiwu ba. Idan na baka adadin bindigogi zaka iya kaiwa Ingila? Ba za ku iya ba, saboda tsaro a ankare yake.''

Malamin ya ba da shawarar a sake fasalin tsarin tsaron Najeriya a matsayin wani bangare na matakan duba ‘yan fashi.

Gumi: Makiyaya suna satar yara ne kawai don kudi, sun fi yan IPOB

A gefe guda, Ahmad Gumi, malamin addinin Islama, ya ce rashin adalci ne idan aka kwatanta ayyukan makiyaya da na 'yan asalin yankin Biafra (IPOB).

Malamin, wanda aka san shi da samun damar zama da yan fashi da makami, ya ce laifukan makiyaya ko kusa basu kai na IPOB.

Da yake magana a shirin gidan talabijin na Arise TV a ranar Laraba, Gumi ya yi kira da adalci a wajen kwatanta kungiyoyin biyu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel