Najeriya za ta ci gaba da zama kasa daya da ba za ta rabe ba, Ganduje
- Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa babu wani yanayi da zai sa Najeriya ta rabu duk da kiran da wasu kungiyoyi ke yi na neman ballewa
- Gwamnan na Kano ya ce mafi yawan mutanen da ke kira da a wargaza kasar ba su shaida yakin basasa ba
- A halin yanzu, ya yi kira ga kowa da kowa ya hada hannu ya ga yadda za a ciyar da kasar gaba ba tare da wata matsala ba
Gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya maida martani game da cece-kuce da ake yi a duk fadin kasar inda wasu mutane ke kira ga cin gashin kai.
A cewar gwamnan, kasar ba za ta rabu ba duk da matsaloli daban-daban da ake fuskanta. Ya ce Najeriya za ta ci gaba da kasancewa tsintsiya madaurinki daya.
KU KARANTA KUMA: Buhari ba zai yi murabus ba, zai cika wa’adinsa, Fadar shugaban kasa ta bayyana
Ya bayyana hakan ne lokacin da yake zantawa da Jaridar Nigerian Tribune.
Ya ce:
“Ina da cikakken yakinin cewa Najeriya ba za ta rabe ba, koda kuwa tana fuskantar kalubale masu girma. Ina da yakinin cewa Najeriya za ta ci gaba da kasancewa kasa daya tilo. Ba na son yin tsokaci kan wadanda ke kira ga raba kasar saboda matasa ne da ba su san yakin basasa ba."
Da yake ci gaba, gwamnan ya yaba wa kungiyar Ohanaeze Ndigbo saboda nesanta kanta daga tashin hankalin masu neman kafa kasar Biyafara.
KU KARANTA KUMA: Jam’iyyar PDP ta yi babban rashi na dan majalisarta a Nasarawa, ya sauya sheka zuwa APC
Ganduje ya ce:
"Ina da kwarin gwiwa domin a makon da ya gabata, Ohanaeze Ndigbo ta ce ba sa cikin masu neman kafa kasar Biyafara; sun kasance masu son Najeriya daya. Afenifere, Kungiyar dattawan Arewa da kuma kungiyar arewa ta tsayika, duk sun ce na Najeriya daya ce."
A halin yanzu, gwamnan ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su yi kokarin tabbatar da hadin kan kasar.
"Don haka, ina kira ga dukkan bangarorin yankin da su hadu su gano yadda za mu iya sauya bambancinmu zuwa ga tabbatar da hadin kan kasar nan. Abin da kawai muke bukata shi ne mu girmama bambance-bambancen da ke tsakaninmu tare da sauya kalubalenmu zuwa hadin kai. Idan Allah Ya so mu zama addini daya, dukkanmu za mu zama addini daya. Idan Allah yana so mu zama jemagu mu yi ta shawagi a duk fadin kasar, za mu zama jemagu. Don haka, ya kamata mu manta da bambance-bambancen da ke tsakaninmu kuma mu zama dunkulalliya a matsayin daya."
Gwamna Ganduje Ya Sha Alwashin Ƙarasa Wani Muhimmin Aiki da Kwankwaso Ya Gaza
A gefe guda, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano, ranar Talata, ya sha alwashin ƙarasa aikin hanyar Gorondutse – Jakara wadda tsohon gwamnan jihar, Rabiu Kwankwaso ya fara, kamar yadda vanguard ta ruwaito.
Hanyar wadda ta taso daga Gorondutse/Aminu Kano zuwa jakara an raɗa mata suna 'Sheikh Mahmud Salga' kuma gwamnatin tsohon gwamna, Rabi'u Kwankwaso ce ta fara aikin a zangon mulki na biyu.
Ganduje ya ɗauki wannan alƙawari ne yayin buɗe biki da aka yi wa take da 'Makon tsaftace jihar Kano' a Jakara.
Asali: Legit.ng