Zargin zambar N7.1bn: Kotun Abuja ta sanar da ranar da za a sake gurfanar da tsohon gwamna, Orji Uzor Kalu

Zargin zambar N7.1bn: Kotun Abuja ta sanar da ranar da za a sake gurfanar da tsohon gwamna, Orji Uzor Kalu

  • Rahotannin da ke shigowa na nuna cewa tsohon gwamnan jihar Abia, Orji Kalu, ya kalubalanci yunkurin da EFCC ke yi na sake gurfanar da shi kan rashawa
  • Hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa ta zargi tsohon gwamnan da wawure biliyoyin nairori a lokacin da ya ke gwamna
  • Kalu ya ce kasancewar an gurfanar da shi, an same shi da laifi, an kuma yanke masa hukunci, hakan na iya zama hukunci sau biyu a gare shi kan tuhuma daya

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta sanya ranar 2 ga watan Yuli a matsayin ranar da za a saurari karar da ke neman a dakatar da sake shari’ar tsohon gwamnan jihar Abia, Orji Uzor Kalu, kan zargin zamba.

Jaridar Guardian ta ruwaito cewa bangarorin da ke karar sun sanar da kotun a ranar Laraba, 23 ga watan Yuni, cewa sun shigar da karar su.

KU KARANTA KUMA: Gumi: Makiyaya suna satar yara ne kawai don kudi, sun fi yan IPOB

Zargin zambar N7.1bn: Kotun Abuja ta sanar da ranar da za a sake gurfanar da tsohon gwamnan, Orji Uzor Kalu
Orji Uzor Kalu na neman kotu ta hana EFCC sake gurfanar da shi Hoto: Orji Uzor Kalu
Asali: Facebook

Lauyan da ke kare tsohon gwamnan, Farfesa Awa Kalu (SAN) ya fada wa kotun cewa wadanda ake karar sun gabatar masa da takardunsu na kalubalantar lamarin.

Alkalin ya karbe ragamar shari’ar

PM News ta ruwaito cewa alkalin, Mai shari’a Inyang Ekwo, a hukuncinsa ya ce tunda dukkan bangarorin sun shiga lamuran kotun ta karbe ragamar shari’ar.

Ekwo ta dage sauraron karar har sai ranar 2 ga watan Yuli domin yanke hukunci.

KU KARANTA KUMA: Najeriya za ta ci gaba da zama kasa daya da ba za ta rabe ba, Ganduje

Badakala: Shugaban EFCC Ya Ci Alwashin Gurfanar da Orji Kalu

A baya mun ji cewa Shugaban hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC), Abdulrasheed Bawa, ya sha alwashin cewa hukumar za ta sake gurfanar da tsohon gwamnan jihar Abia, Orji Kalu.

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa Bawa ya bayyana hakan ne lokacin da yake zantawa da manema labarai a Abuja a ranar Alhamis, 17 ga watan Yuni.

Kalu, wanda yanzu haka dan majalisar dattijai ne, Kotun Koli ta sake shi a kan ka'idoji bayan an same shi da laifin satar biliyoyin nairori lokacin da yake gwamnan jihar Abia tsakanin 1999-2007.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng