Labari Cikin Hotuna: Shugaba Buhari Ya Gana da Gwamna Atiku Bagudu Kan Ɗaliban FGC da Aka Sace

Labari Cikin Hotuna: Shugaba Buhari Ya Gana da Gwamna Atiku Bagudu Kan Ɗaliban FGC da Aka Sace

  • Shugaba Buhari ya gana da gwamnan Kebbi, Atiku Bagudu, kan yanayin tsaron da jiharsa ke ciki
  • Gwamna Bagudu yayi wa shugaban bayanin halin da ake ciki, musamman sace ɗaliban FGC Birnin Yauri
  • Wannan ganawa ta gudana ne a fadar shugaban ƙasa dake Abuja ranar Talata da daddare

Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya gana da gwamna Atiku Bagudu na jihar Kebbi kan ɗaliban makarantar sakandiren gwamnatin tarayya da aka sace a jihar.

Shugaban ya gana da gwamnan ne domin jin yadda lamarin ya faru da kuma inda aka kwana akan lamarin.

KARANTA ANAN: Babu Wata Matsalar Tsaro da Ta Fi Matsalar Yunwa Hatsari, Zulum Ya Koka

Gwamnan Bagudu ya yiwa Buhari bayanin halin da ake ciki da kuma matakan da aka fara ɗauka domin kuɓutar da ɗaliban

Shugabannin biyu sun gana ne da daren jiya Talata a fadar shugaban Ƙasa dake Abuja, kamar yadda Buhari Sallau ya rubuta a shafinsa na facebook.

Hotunan Shugaba Buhari da Atiku Bagudu

Shugaba Buhari Ya Gana da Gwamna Atiku Bagudu
Labari Cikin Hotuna: Shugaba Buhari Ya Gana da Gwamnan Atiku Bagudu Kan Ɗaliban FGC da Aka Sace Hoto: Buhari Sallau FB fage
Asali: Facebook

Shugaba Buhari Ya Gana da Gwamna Atiku Bagudu
Labari Cikin Hotuna: Shugaba Buhari Ya Gana da Gwamnan Atiku Bagudu Kan Ɗaliban FGC da Aka Sace Hoto: Buhari Sallau FB Fage
Asali: Facebook

Shugaba Buhari tare da Atiku Bagudu
Labari Cikin Hotuna: Shugaba Buhari Ya Gana da Gwamnan Atiku Bagudu Kan Ɗaliban FGC da Aka Sace Hoto: Buhari Sallau FB fage
Asali: Facebook

A makon da ya gabata ne yan bindigan suka kai hari makarantar FGC Birnin Yauri, inda suka yi awon gaba da wani adadi na ɗalibai da malamai guda huɗu.

KARANTA ANAN: Duk Masu Ɗaukar Makami Su Yaƙi Najeriya Zasu Ɗanɗana Kuɗarsu, Shugaba Buhari Ya Jaddada

Legit.ng hausa ta tattaro muku wasu daga cikin ra'ayoyin mutane kan wannan ganawar da aka yi.

Abdulganiyu Jimoh, yace:

"Wannan yazo lokacin da ya dace domin yanzun jami'an tsaron mu na ɗaukar matakin da ya dace da yan ta'addan."

Usman Mu'azu Ksauri, yace:

"Masha Allah, Allah yasa a tattauna alkairi."

A wani labarin kuma Yan Bindiga Sun Saki Hotunan Halin da Malamai, Ɗaliban Kebbi Ke Ciki

Yan bindigan da suka yi awon gaba da ɗalibai a FGC Birnin Yauri sun saki hotunan waɗanda suka kama.

A makon da ya gabata ne maharan suka dira makarantar sakandiren, inda suka yi awon gaba da wani adadi na ɗalibai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262