Babu Wata Matsalar Tsaro da Ta Fi Matsalar Yunwa Hatsari, Zulum Ya Koka
- Gwamna Zulum na jihar Borno, ya koka matuƙa kan matsalar rashin abinci dake fuskantar jiharsa
- Gwamnan yace matsalar rashin abinci tafi tsanani fiye da matsalar tsaro da ake fama da ita a yankin
- Ya kuma ƙara da cewa NGO sun yi matuƙar ƙoƙari wajen kai ɗauki yankin amma basu taimakawa da abinci
Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umaru Zulum, ya bayyana cewa jihar sa na gab da faɗawa cikin matsananciyar yunwa matuƙar ba'a bar manoma sun koma gonakin su ba, kamar yadda premium times ta ruwaito.
KARANTA ANAN: Wani Kwamishina Ya Rigamu Gidan Gaskiya, Gwamna Ya Bayyana Ranar Hutu Saboda Jimami
Zulum ya shaida wa BBC Hausa cewa yanayin ya fara munana sabida dubbannin yan gudun hijira da suka koma gidajen su ba su da abincin da zasu ci kuma an hana su noma a gonakinsu.
Zulum, yace:
"Babu wata matsalar tsaro da ta fi matsalar yunwa hatsari, idan babu abincin da za'a ci, to abubuwa marasa kyau ka iya faruwa. A halin yanzun mun shiga yanayin da idan ba'a ƙyale manoma sun yi aikin noman su ba to zasu iya kashe junan su domin su samu abinci."
"Yanzun jihar mu na fuskantar rashin abinci, ba zai yuwu mu jira sai komai ya dai-daita ba sannan mutane su cigaba da noma, kamata yayi mu yi maganin hare-haren Boko Haram da kan mu. Ba zamu amince yan bindiga 5-10 su tada garin dake da mutane sama da 10,000."
"Bai kamata mubar mutane su mutu da yunwa ba, kuma yayan mu basa zuwa makaranta, hakan bai kamata ya cigaba da faruwa ba."
KARANTA ANAN: Gwamna Ganduje Ya Sha Alwashin Ƙarasa Wani Muhimmin Aiki da Kwankwaso Ya Gaza
NGO suna bakin ƙoƙarinsu amma yaudarar su ake, inji Zulum
Gwamnan ya ƙara da cewa ƙungiyoyi masu zaman kansu dake taimakawa a jihar, sun yi matuƙar ƙoƙari amma yanzun basu taimakawa da abinci saboda ana yaudararsu.
Mr. Zulum ya koka kan cewa mutane sun koma asalin gidajensu domin su noma gonakin su, kuma su cigaba da kasuwancin su.
A wani labarin kuma Wasu Yan Bindiga Sun Hallaka Jigon Jam'iyyar APC a Jihar Ondo
Wasu mutane ɗauke da bindiga sun farmaki ɗaya daga cikin mambobin kwamitin zartarwa na APC a Ondo.
Hon Dele Isibor, ya rasa ransa ne ranar Litinin sabida raunukan da yaji a harin da yan ta'addan suka kai mishi.
Asali: Legit.ng