Buhari ba zai yi murabus ba, zai cika wa’adinsa, Fadar shugaban kasa ta bayyana

Buhari ba zai yi murabus ba, zai cika wa’adinsa, Fadar shugaban kasa ta bayyana

  • Babafemi Ojudu, mai baiwa shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin siyasa, ya bayyana cewa shugaba Buhari ba zai bar ofis ba har sai 2023
  • Ojudu ya bayyana hakan ne a garin Abuja a ranar Talata 22 ga watan Yuni, a yayin gabatar da wani littafi da Abdullahi Haruna ya rubuta domin girmama shugaban
  • Hadimin shugaban kasar ya lura cewa tashin hankali kan neman yayi murabus ko a cire shi ba sabon abu ba ne ga shugaban na Najeriya

Fadar shugaban kasa ta mayar da martani game da kiraye-kirayen da aka yi a wurare daban-daban na neman murabus din Shugaba Muhammadu Buhari kan yawaitar kashe-kashe da sace-sacen mutane a kasar.

Jaridar The Punch ta rahoto cewa mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin siyasa, Babafemi Ojudu, a ranar Talata, 22 ga watan Yuni, ya ce duk da kiranye-kirayen, shugaban kasar zai kammala wa’adinsa ba tare da lahani ba.

KU KARANTA KUMA: Ko kadan ba na jin tsoron mutuwa – Gwamna Babagana Zulum

Buhari ba zai yi murabus ba, zai cika wa’adinsa, Fadar shugaban kasa ta bayyana
Babafemi Ojudu ya bayyana cewa sai Shugaba Buhari ya kammala wa'adinsa sannan zai sauka daga mulki Hoto: Femi Adesina
Asali: Facebook

Legit.ng ta tattaro cewa Ojudu yace idan Buhari ya gama, zai mika mulki ga wani bawan Allah wanda zai karfafa nasarorinsa.

Tsohon sanatan ya yi magana ne yayin da yake wakiltar mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo a yayin gabatar da wani littafi, 'Buhari In Us,' wanda Abdullahi Haruna ya rubuta a Abuja a ranar Talata, 22 ga Yuni.

KU KARANTA KUMA: Jami'an tsaro sun tasa keyar tsohon dan majalisa Farouk zuwa gidan yarin Kuje

A cewarsa, kamfen don murabus dinsa ko cire shi ba sabon abu ba ne ga shugaban kasar kamar yadda aka yi irin wannan hargitsi a lokacin yana Shugaban kasa na soja.

Ojudu ya ce:

“Ga wadanda basa nan daga cikinku a lokacin zuwansa na farko, ya jajirce kamar yadda yake yanzu. Ya kulle dukkan gurbatattun ‘yan siyasa. Makiyan wannan kasar a lokacin sun fara kamfe a kan sa kuma ta yi karfi yanzu kamar yadda take a lokacin."

Jaridar Vanguard ta kuma ruwaito cewa gwamnatin tarayya ta bayyana cewa Buhari ba zai yi murabus ba saboda kalubalen rashin tsaro.

Gwamnatin ta bayyana cewa ana magance kalubalen tsaro gaba daya.

Lawan: Bayan saukar mulkin Buhari, akwai yuwuwar APC ta fuskanci kalubale

A wani labarin, Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ya ce jam'iyyar APC za ta iya fuskantar kalubale bayan sauka mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari a 2023, sai dai idan an kai taimakon gaggawa.

Lawan ya bada wannan jan kunnen ne a daren Litinin a jawabin da yayi na rufe taron farko na matasan jam'iyyar APC wanda aka yi a Abuja, Daily Nigerian ta ruwaito.

Kamar yadda yace, dole ne jam'iyyar ta fara shiri domin rike kyawawan ayyukan wannan mulkin ta yadda za ta tabbatar da cewa an mika mulki hannun matasan jam'iyyar APC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel