Ko kadan ba na jin tsoron mutuwa – Gwamna Babagana Zulum

Ko kadan ba na jin tsoron mutuwa – Gwamna Babagana Zulum

  • Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno ya bayyana cewa sam shi ba ya tsoron mutuwa shi ya sa yake shiga wuraren da Boko Haram suka kai hare-hare
  • A cewar Zulum, Allah ne ya bashi mulki kuma da shi ya dogara saboda haka bashi da sauran fargaba domin duk abun da ya so ne yake kasancewa
  • Ya kuma bayyana cewa da bai zuwa wuraren da hare-hare ke faruwa da yanzu babu wasu garuruwa kamar irinsu Dikwa, Baga da sauransu

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya bayyana cewa shi ba ya tsoron mutuwa shi ya sa yake shiga duk wuraren da mutanen da rikicin Boko Haram ya raba da gidajensu suke zaune.

Zulum ya fadi hakan ne a wata hira da yayi da sashin Hausa na BBC, inda ya kuma bayyana cewa shi ya dogara ne ga Allah wanda ya bashi mulki.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Kungiyar NLC za ta sake komawa yajin aiki a Kaduna

Ko kadan ba na jin tsoron mutuwa – Gwamna Babagana Zulum
Gwamna Babagana Zulum ya ce ko kadan ba ya jin tsoron mutuwa Hoto: BBC.com
Asali: UGC

Da aka tambaye shi kan dalilin da ya sa yake zuwa yankuna masu hatsari wadanda aka kwato daga hannun 'yan Boko Haram, har ma yakan kwana, sai Gwamna Zulumm ya ce:

"Mutane su gane cewa raina sai lokacin da Allah ya ce zai fita sannan zai fita. Kuma babu wani dan Adam da bai son ran shi, amma ka duba dubban mutanen da suke shan wahala.
“Ka tabbatar da cewa duk inda Boko Haram ya zo ya ci mutane, ni koma menene zan shiga, mun tafi Damasak, da bamu tafi Damasak bame zai faru? Kuma a mota na tafi. Babu wani magana da muka yi na tafi da mota, wasu ma ba za su iya tafiya da mota ba.
“Bana so na kama sunan mutane, amma har mun je mun kwana, mun tabbatar cewa mutanen da suka yi kaura suna zuwa Nijar muna maida su sun kai mutane dubu daya.
“Toh idan mun ji tsoro mun koma ina wadannan mutanen za su zauna da mata da yara, mace ta haihu a hanya, wasu kuma an sake kama su a hanya. Kamar garin Dikwa da naje yanzu haka akwai mutane dubu dari uku, ina za su tafi? Shiyasa ba za mu ji tsoro ba, Allah zai kiyaye mu kuma idan kwana ya kare Allah ya sa mu cika da imani.”

KU KARANTA KUMA: Biloniya kike aure: An yi cece-kuce yayin da Zahra Buhari ta ce aure na nufin soyayya mara iyaka a gare ta

Kan cewa ko dai yana shiri ne na musamman, Zulum ya ce:

“Babu wani abu, sai dai dogara da Allah, duk abunda yace zai faru sai ya faru, babu wani abu idan dai ka dogara da Allah shikenan."

Game da cewar wasu basa so yana shiga irin wuraren saboda gudun tsautsayi, gwamnan ya ce:

“Ai ina jin maganarsu nayi sauki idan ba haka ba idan ni naje zan yi kwana har sati biyu zuwa uku ma. Kowane lokaci zan tafi kuma idan aka ce mun jirgi nab a zan tafi ba. Zan je Damatar suka ce mun jirgi nace b azan tafi ba dole na tafi na bi hanyan nan saboda mutane su bi.
“Wato ba da karfi na bane, amma yanzu da muka shiga mulki da mun zauna a cikin daki mun rufe da yanzu babu Baga, babu Dikwa, ba magwar yanzu, dole mu tabbatar cewa mun yi hakuri kuma Allah ne ya bamu mulki, kuma idan Allah ya baka mulkin nan zai baka abubuwa da yawa, idan ka dogara da shi zai ude maka hanya.”

‘Ka yi matukar burge ni’, inji Buhari bayan da ya bude ayyuka 7 na Gwamna Zulum

A wani labarin, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya gagara boye farin cikinsa a ranar Alhamis a Maiduguri bayan da ya kaddamar da ayyuka bakwai cikin 556 da Gwamnan Jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum, ya aiwatar cikin shekara biyu da ya yi a kan karaga.

Gwamna Zulum da kansa ya bayyana haka a jawabin da ya saki ranar Alhamis a shafinsa.

Buhari ya kara da cewa zaga inda na bude wasu daga cikin ayyukan da gwamnatin Zulum ta gudanar cikin shekara biyu tana mulki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel