Jami'an tsaro sun tasa keyar tsohon dan majalisa Farouk zuwa gidan yarin Kuje
- Jami'an tsaro sun tasa keyar tsohon dan majalisar wakilai, Farouk Lawan zuwa gidan yari
- A ranar Talata ne babbar kotun tarayya ta yanke masa hukuncin shekaru bakwai a gidan maza
- Alkali Angela ta yanke hukuncin bayan kama shi da laifuka uku da suka hada da karbar rashawa
Bayan shekaru tara da majalisar wakilai ta rincabe da bincike kan wata damfarar tallafin man fetur, shugaban kwamitin wucin-gadi na wancan lokacin, Farouk Lawan, an yanke masa hukuncin shekaru bakwai a gidan yari kan karbar cin hanci daga biloniya Femi Otedola, mamallakin daya daga cikin kamfanonin da ake bincika.
Wata babbar kotun tarayya dake zama a Apo wacce ta samu shugabancin mai shari'a Angela Otaluka a ranar Talata, ta kama Lawan da laifuka uku da ake zarginsa dasu tun a 2012, Daily Trust ta wallafa.
KU KARANTA: Masu jiran tarwatsewar kasar Najeriya zasu sha kunya, Yemi Osinbajo
KU KARANTA: Bidiyon 'yan sanda suna gudun ceton rai bayan jin sauti daga makabarta
Wasu majiyoyi kusa da tsohon dan majalisar sun ce an tasa keyarsa zuwa gidan yarin dake Kuje a Abuja.
Wata majiya da ta bukaci a sakaya sunanta ta tabbatar da cewa an kai Lawan gidan yarin jim kadan bayan kotun ta yanke masa hukunci.
"Tabbas, an kawo shi nan kai tsaye daga dakin kotun. Daga yau, ya fara zaman gidan yarin da aka yanke masa kuma zai cigaba har sai ya kammala ko kuma ya daukaka kara kuma yayi nasara," yace.
Yayin da aka yankewa Lawan hukunci saboda karbar rashawa, ba a gabatar da wani laifi ba game da wanda ake zargin ya bada cin hancin, Otedola, lamarin da lauyoyi ke ta bayani kuma shari'a ta gamsu da hakan.
Otedola da kanshi yayin shari'ar yace kudin da ya baiwa Lawan cin hanci ba nashi bane, hukumar tsaro ta farin kaya ce ta bashi domin ya bada kuma aka samu Lawan ya karba, Daily Trust ta ruwaito.
An yankewa tsohon dan majalisar wakilan hukunci ne sakamakon karbar cin hanci na $500,000 daga femi Otedola.
A wani labari na daban, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarci Babatunde Fashola, ministan ayyuka da gidaje, Abubakar Malami, Antoni janar na tarayya da su tattauna da Twitter kan dakatar da ita da aka yi a Najeriya.
Gwamnatin tarayya ta haramta Twitter a Najeriya tun bayan zargin kafar sada zumuntar da aka yi da katsalandan, Daily Trust ta wallafa.
Duk da matsantawa da aka yi daga kasashen ketare da kungiyoyi, gwamnatin Buhari ta cigaba da tsayuwa kan matsayarta.
Asali: Legit.ng