Lawan: Bayan saukar mulkin Buhari, akwai yuwuwar APC ta fuskanci kalubale

Lawan: Bayan saukar mulkin Buhari, akwai yuwuwar APC ta fuskanci kalubale

  • Ahmad Lawan, shugaban majalisar dattawa yace akwai babban kalubale gaban APC idan Buhari ya kammala wa'adin mulkinsa
  • Shugaban majalisar yace ya zama dole jam'iyyar ta fara shiri domin tabbatar da cigaban ingantaccen mulki irin na Buhari
  • Lawan ya ce tabbas jam'iyyar APC ta yi asarar shekaru hudu na farkon mulkinta amma yanzu zata gyara ta hanyar saka matasa da mata a sahun gaba

Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ya ce jam'iyyar APC za ta iya fuskantar kalubale bayan sauka mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari a 2023, sai dai idan an kai taimakon gaggawa.

Lawan ya bada wannan jan kunnen ne a daren Litinin a jawabin da yayi na rufe taron farko na matasan jam'iyyar APC wanda aka yi a Abuja, Daily Nigerian ta ruwaito.

Kamar yadda yace, dole ne jam'iyyar ta fara shiri domin rike kyawawan ayyukan wannan mulkin ta yadda za ta tabbatar da cewa an mika mulki hannun matasan jam'iyyar APC.

KU KARANTA: Luguden wuta: Dan sanda ya sheke mutum 5, 4 sun jigata sakamakon tatil da yayi da giya

Lawan: Bayan saukar mulkin Buhari, akwai yuwuwar APC ta fuskanci kalubale
Lawan: Bayan saukar mulkin Buhari, akwai yuwuwar APC ta fuskanci kalubale. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Uwa ta gwangwaje danta da mota BMW yayin cikarsa shekaru 10 a duniya

APC tayi asarar shekaru hudu

"A gaskiya APC ta yi asarar shekaru hudu masu muhimmanci kuma a wannan shekarun ne ya dace mu gamsar da 'yan Najeriya cewa sun yanke hukuncin da ya dace lokacin da suka kori PDP a 2015.

"Mene gare mu yanzu? Mu jam'iyya daya ce kuma muke rike da mukamai daban-daban na gwamnati. Ya dace a ce manufofinmu daya ne. Shirye-shiryenmu da kuma ayyukanmu ya dace su zama daya.

"Matukar kana APC, ya dace a ce shirinka da ayyukanka na ganin samun nasara ne," Lawan yace kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Gyaran kundin tsarin mulki

Shugaban majalisar dattawa ya kara da bayyana cewa wannan gyaran kundun tsarin mulkin zai bada fifiko wurin baiwa matasa dama a shugabanci.

Yayi bayanin cewa amfanin abun shine ganin cewa an mika mulki ga masu tasowa ta yadda zasu fada sha'anin mulki kai tsaye.

"Ba abokan hamayya suke bada mulki ba. A lokacin da bamu kan mulki ko muka samu mulki, wata jam'iyyar ce PDP ke juya kasar.

“Babu yadda za a yi a bamu mulki kai tsaye, amma jama'ar Najeriya ne suka fatattaketa da kuri'unsu.

"Ina tunanin zai fi dacewa kuma za a fi samun sakamakon da ake so idan aka samu yawaitar matasa da mata a lamarin shugabanci." Lawan yace.

A wani labari na daban, Gwamna Abubakar Sani Bello na jihar Neja ya samu ganawa da iyayen dalibai 136 na makarantar Islamiyya ta Salihu Tanko dake Tegina, wadanda aka sace a watan da ya gabata.

Gwamnan ya shilla kasar waje bayan sa'o'i kadan da sace yaran, yayin da mataimakinsa ya dinga kokarin ganin an sakosu, Daily Trust ta ruwaito.

Bayan dawowarsa kasar, Bello ya kaddamar da kungiyar sintiri ta musamman domin magance matsalar tsaro da ke cigaba da gawurta a jihar kuma ya karasa Tegina domin ganawa da iyayen yaran.

Asali: Legit.ng

Online view pixel