Majalisa za ta binciki gwamnatin Buhari kan shirin farfado da tattalin arziki

Majalisa za ta binciki gwamnatin Buhari kan shirin farfado da tattalin arziki

  • Majalisar dattijai ta bayyana cewa, za ta binciki ministar kudi kan shirin farfado da tattalin arziki
  • Rahotanni sun bayyana cewa, majalisar ta ce ta ji shuru game da yadda shirin ke tafiya bayan wucewarsa
  • Hakazalika, an bukaci kwamitocin da abun ya shafa da su tattauna tare da ministar don sanin in da aka kwana

Majalisar dattijai a ranar Talata ta tambayi kwamitocinta a kan Tsarin Kasa; Banki, Inshora da sauran Cibiyoyin Kudi.

Ciki har da na Sufurin Ruwa; Sufurin Kasa da Ayyuka da Wuta don tattaunawa tare da Ministar Kudi, Kasafin Kudi da Tsare-Tsaren Kasa, Zainab Ahmed, kan shirin Farfado da Tattalin Arzikin Gwamnatin Tarayya na 2017 zuwa 2020, Daily Trust ta ruwaito.

Wannan ya biyo bayan wani yunkuri ne "kan bukatar tantance tasiri kan ayyukan Tattalin Arziki da Ci Gaban Kasa (ERGP) na 2017 zuwa 2020" wanda Sanata Abdu Suleiman Kwari ya dauki gabatarwa majalisa.

KU KARANTA: Da dumi-dumi: Bayan ritaya, an tura burutai wata kasa a matsayin ambasada

Majalisar dattawa za ta binciki tsarin Buhari na farfado da tattalin arziki
Majalisar dattijai ta Najeriya | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Kwari ya ce ERGP, wanda yanzu haka ya jima da wucewa, ba za a iya cewa ya cimma burin farfadowa da inganta tattalin arziki da ake so ba.

Ya kasance akwai bukatar yin cikakken bincike game da aikin tsarin don tabbatar ko ya cika burin da ake bukata.

Ya tuna cewa Shugaban kasa, Manjo Janar Muhammadu Buhari, (mai ritaya), ya kaddamar da shirin a watan Afrilu na 2017 don tabbatar da ci gaban tattalin arzikin kasa gaba daya, in ji jaridar Punch.

Kwali ya ce:

“An tsara shirin ne don cimma nasarar sauya tsarin tattalin arziki tare da karfafawa kan inganta bangarorin gwamnati da masu zaman kansu na tattalin arzikin Najeriya."

KU KARANTA: 'Yan sanda sun kame tsagerun IPOB 60 dake kai hare-hare da kone ofisoshin INEC

Hotunan yadda ambaliyar ruwa ta mamaye majalisar dokoki ta kasa

A wani labarin, Ruwa ya mamaye harabar Majalisar Dokoki ta Kasa dake Abuja, da safiyar yau Talata, Daily Trust ta ruwaito.

Lamarin abin kunya ya faru ne yayin da ake ruwan sama kamar da bakin kwarya a babban birnin kasar.

Rahotanni sun ce rufin ginin Majalisar Dokokin ya fara yoyo ne yayin da ake ruwan sama kamar da bakin kwarya a ranar Talata.

Babban zaure wanda ke kaiwa zuwa zauren majalisar dattijai da na wakilai ya cika da ruwa saboda ruwan sama makil. Cibiyar 'yan jaridu inda 'yan rahoto ke zama don sa ido kan zaman majalisar bai tsira daga ambaliyar ba, The Cable ta tattaro.

Asali: Legit.ng

Online view pixel