Da dumi-dumi: Bayan ritaya, an tura burutai wata kasa a matsayin ambasada

Da dumi-dumi: Bayan ritaya, an tura burutai wata kasa a matsayin ambasada

  • Gwamnatin Buhari ta tura Janar Burutai zuwa jamhuriyar Benin a matsayin jakadan Najeriya
  • Hakazalika ta tura Geoffrey Onyeama a matsayin jakadan Najeriya zuwa jamhuriyar Kamaru
  • A baya an sanar da nadin tsoffin hafsoshin tsaron Najeriya a matsayin jakadun Najeriya

Tsohon hafsan hafsoshin soja, Lt.Gen. Tukur Yusufu Buratai (rtd), an tura shi Jamhuriyar Benin a matsayin jakada, Daily Trust ta ruwaito.

Yayin da Janar Abayomi Gabriel Olonisakin (rtd), tsohon Babban hafsan hafsoshin tsaro, aka nada a matsayin shugaban mishan zuwa kasar Kamaru.

A wani takaitaccen bikin da aka yi a Abuja ranar Talata, Ministan Harkokin Wajen, Geoffrey Onyeama, ya gabatar da wasikun amincewa da nadin tsofaffin shugabannin na tsaro.

KU KARANTA: Ba sauran bin dogon layi: INEC ta saukaka hanyar yin rajistar masu zabe

Da dumi-dumi: An nada Burutai jakadan Najeriya a kasar Benin
Janar Tukur Yusuf Burutai mai ritaya | Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Mista Kimiebi Ebienfa, jami'in yada labarai na ma'aikatar ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa.

Sai dai, sanarwar ta yi shiru a kan nadin sauran tsofaffin shugabannin hafsoshin na tsaro.

An ruwaito cewa a ranar 4 ga Fabrairu, 2021, Shugaba Muhammadu Buhari ya nada tsofaffin shugabannin a matsayin jakadu na Najeriya, The Guardian ta ruwaito.

Nadin nasu na jakadanci ya haifar da fushin tsakanin jama’a, tare da yin kira ga Majalisar Dattawa da ta yi watsi da nade-naden nasu.

Duk da nuna fushin, Majalisar Dattawa, a ranar 23 ga Fabrairu, 2021, ta tabbatar da nadin nasu.

KU KARANTA: Shugabannin kudu da na arewa sun yabawa gwamnonin kudu bisa tir da IPOB

Bayan Shekaru 6, Buhari ya yi sabbin nade-nade a hukumar EFCC

A wani labarin, Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da nadin George Abangeekpungu a matsayin sakataren hukumar yaki da masu yiwa tattalin arziki zagon kasa (EFCC).

Nadin na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin ofishin babban lauyan Najeriya da ma'aikatar shari'a ta kasa, Umar Jibrila Gwandu ya sanyawa hannu a Abuja, Daily Nigerian ta ruwaito. A cewar sanarwar, wa'adin sabon nadin zai kasance na shekara biyar ne.

Hakanan an nada Mambobin Kwamitin na EFCC da suka hada da Luqman Muhammad (Kudu maso Kudu), Anumba Adaeze (Kudu maso Gabas), Alhaji Kole Raheem Adesina (Arewa ta Tsakiya) da Alhaji Yahya Muhammad (Arewa maso Gabas).

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.