Abun takaici: Hotunan yadda ambaliyar ruwa ta mamaye majalisar dokoki ta kasa

Abun takaici: Hotunan yadda ambaliyar ruwa ta mamaye majalisar dokoki ta kasa

  • Wani abun takaici ya faru a zauren majalisar dokoki ta Najeriya a yau yayin zaman majalisa
  • An tafka ruwa kamar da bakin kwarya, lamarin da ya kai ga fashewar rufin sama na majalisar
  • Ruwa yayi ambaliya yayin da ruwan ya malala har zuwa cikin farfajiyar majalisar dake Abuja

Ruwa ya mamaye harabar Majalisar Dokoki ta Kasa dake Abuja, da safiyar yau Talata, Daily Trust ta ruwaito.

Lamarin abin kunya ya faru ne yayin da ake ruwan sama kamar da bakin kwarya a babban birnin kasar.

Rahotanni sun ce rufin ginin Majalisar Dokokin ya fara yoyo ne yayin da ake ruwan sama kamar da bakin kwarya a ranar Talata.

KU KARANTA: Ba sauran bin dogon layi: INEC ta saukaka hanyar yin rajistar masu zabe

Abun takaici: Hotunan yadda ambaliyar ruwa ta mamaye majalisar kasa
Ambaliyar ruwa a farfajiyar majalisar dokoki ta kasa | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Babban zaure wanda ke kaiwa zuwa zauren majalisar dattijai da na wakilai ya cika da ruwa saboda ruwan sama makil.

Cibiyar 'yan jaridu inda 'yan rahoto ke zama don sa ido kan zaman majalisar bai tsira daga ambaliyar ba, The Cable ta tattaro.

Ma'aikatan tsafta na majalissar sun yi gwagwarmaya fiye da mintuna 20 don kwashe ruwan da ya cike wajen.

Amma duk da halin da ake ciki bai hana ‘yan majalisar zama ba.

A shekarar 2019, majalisar dokokin kasa ta ware kasafin kudi har naira biliyan 42 domin gyara katafaren ginin.

Lamarin ya haifar da suka yayin da wasu 'yan Najeriya suka fusata da kudin da aka ware don gyaran.

Kalli hotunan:

Abun takaici: Hotunan yadda ambaliyar ruwa ta mamaye majalisar kasa
Ambaliyar ruwa a farfajiyar majalisar dokoki ta kasa | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Abun takaici: Hotunan yadda ambaliyar ruwa ta mamaye majalisar kasa
Ambaliyar ruwa a farfajiyar majalisar dokoki ta kasa | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Abun takaici: Hotunan yadda ambaliyar ruwa ta mamaye majalisar kasa
Ambaliyar ruwa a farfajiyar majalisar dokoki ta kasa | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Mai kamfanin BUA, Abdul Samad Rabi'u ya gwangwaje jihohi 4 da tallafin biliyoyi

Majalisar dattawa ta tabbatar da Manjo Janar Farouk Yahaya a matsayin shugaban sojoji

A wani labarin, Majalisar dattijai a ranar Talata ta tabbatar da nadin Manjo Janar Farouk Yahaya a matsayin shugaban hafsan soji (COAS), jaridar Vanguard ta ruwaito.

Tabbatar da Yahaya ya biyo bayan gabatarwa da kuma duba rahoton kwamitin hadin gwiwa na majalisar dattijai kan tsaro da sojoji a zaman majalisa.

Shugaban kwamitin majalisar dattijai kan harkokin tsaro, Sanata Aliyu Wamakko ne ya gabatar da rahoton, jaridar The Nation ta ruwaito.

Janar Yahaya ya kasance yana aiki a matsayin shugaban soji na rikon kwarya bayan rasuwar magabacinsa, Laftanar Janar Ibrahim Attahiru, wanda ya mutu a hatsarin jirgin saman soja a Kaduna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel