'Yan sanda sun kame tsagerun IPOB 60 dake kai hare-hare da kone ofisoshin INEC

'Yan sanda sun kame tsagerun IPOB 60 dake kai hare-hare da kone ofisoshin INEC

  • 'Yan sanda a jihar Ebonyi sun cafke wasu bata gari da ake zargin 'yan kungiyar IPOB ne
  • An kame akalla 60 daga cikinsu, dauke da makamai kuma su ake zargi da kone ofisoshin 'yan sanda
  • Hakazalika an kame su da layu da kunkuru mai rai da bindigogi da alburusai da dama

Rundunar ‘yan sandan jihar Ebonyi ta kama wasu mutane sama da 60 da ake zargi membobin kungiyar nan ce ta Biafra mai neman ballewa daga Najeriya.

Ana zargin mutanen cewa sune suka yi ta kai hare-hare kan ‘yan sanda da kona ofisoshin ‘yan sanda da kuma hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) a jihar ta Ebonyi.

Kwamishinan ‘yan sanda na jihar yace an kwato bindigogi da albarusai da kunkuru mai rai da layu daga hannun wadanda ake zargin.

KU KARANTA: Da dumi-dumi: Bayan ritaya, an tura burutai wata kasa a matsayin ambasada

'Yan sanda sun kame tsagerun IPOB 60 dake kai hare-hare da kone ofisoshin INEC
'Yan kungiyar fafutukar ballewa daga Najeriya ta IPOB | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Wakilin BBC na Legas Umar Shehu Ellema ya tambayi kwamishinan 'yan sandan jihar Ebonyi, Aliyu Garba, ya bayyana makamai da adadin mutane da aka kame.

Ya ce:

"Eh, wajen mutane 63 muka samu. Wadannan mutane mutanen banza ne, dake ta addabanmu, wasu da suke kiran kansu ESN ko IPOB."

A kwanakin baya, rundunar ‘yan sanda a jihar Imo ta ce ta cafke mutane biyar da ake zargi mambobin kungiyar IPOB ne da zargin kisan wani sajan din 'yan sanda, Joseph Nwaka.

Bayanai kan kamun na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sanda a jihar, SP Orlando Ikeokwu ya fitar a Owerri, Premium Times ta ruwaito.

Mista Ikeokwu ya ce an cafke wadanda ake zargin ne a karamar hukumar Isu da ke jihar, tsakanin ranar Alhamis zuwa Juma’a, ta bangaren sashin masu satar mutane da sauran rundunonin rundunar.

Ya ce an kwato bindigar AK 47 da harsasai 15 daga hannun wadanda ake zargin.

KU KARANTA: Gwamnatin Buhari ta fadi dalilan da yasa ba za ta amince da ci gaban Twitter ba

Shugabannin kudu da na arewa sun yabawa gwamnonin kudu bisa tir da IPOB

A wani labarin, Shugabannin arewa da kudancin Najeriya a ranar Lahadi, 20 ga watan Yuni sun goyi bayan matsayar gwamnonin kudu maso gabas da sauran shugabanni a yankin Ibo bisa nacewa kan hada kan kasa tare da nesanta yankin da kiraye-kirayen ballewa daga IPOB.

Da take bayyana goyon baya ga matsayar shugabannin kudu maso gabas, kungiyar koli ta zamantakewar arewa, Arewa Consultative Forum (ACF), da takwararta a shiyyar kudu maso kudu, kungiyar Pan Niger Delta Forum (PANDEF) ta ce Najeriya ta fi kyau a dunkule uwa daya.

Kakakin ACF, Mista Emmanuel Yawe, ya shaida wa jaridar Leadership cewa:

"Idan akwai wata kabila da ta ci gajiyar hadin kan Najeriya, to 'yan kabilar Ibo ne. Idan suka jagoranci ballewar Najeriya, za su haifar da kiyayya mai yawa daga wadanda suke kaunar Najeriya kuma suke son ta ci gaba da kasancewa a dunkule. Dole ne su tafi.”

Asali: Legit.ng

Online view pixel