Wata Jami'a Ta Kori Ɗalibi Ɗan '500-Level' Saboda Ya Soki Gwamna a Facebook

Wata Jami'a Ta Kori Ɗalibi Ɗan '500-Level' Saboda Ya Soki Gwamna a Facebook

  • Jami'ar jihar Akwa Ibom ta sallami ɗalibinta dake shekarar ƙarshe saboda zargin ya ɓata wa gwamnan jihar suna
  • Ɗaliɓin mai suna, Iniobong Ekpo, yayi rubutun zargi a kan gwamnan jihar a dandalin sada zumunta tun shekarar 2019
  • Ekpo na shekararsa ta ƙarshe a sashen karatun koyon aikin gona na jami'ar jihar Akwa Ibom

Hukumar jami'ar jihar Akwa Ibom ta kori ɗalibinta, Iniobong Ekpo, bisa zargin ya zagi gwamnan jihar Emmanuel Udom, a facebook, kamar yadda the cable ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Hana Amfani da Twitter: Lai Muhammed Ya Bankaɗo Wani Asirin Twitter a Gaban Yan Majalisa

Ekpo na shekarar ƙarshe a karatunsa na jami'ar yayin da aka sallame shi saboda laifin da ya aikata tun shekarar 2019.

Jami'ar jihar Akwa Ibom
Wata Jami'a Ta Kori Ɗalibi Ɗan '500-Level' Saboda Ya Soki Gwamna a Facebook Hoto: planet101fm.ng
Asali: UGC

Ɗalibin yayi rubutu ne a dandalin sada zumunta na Facebook, wanda jami'ar take ganin ya saɓa wa dokokinta.

Da farko jami'ar ta dakatar da Ekpo a watan Satumba 2020, kafin ta rubuta masa takardar sallama ɗauke da ranar 9 ga watan Afrilu, 2021.

KARANTA ANAN: Da Duminsa: Kotun ECOWAS Ta Dakatar da Gwamnatin Buhari Daga Cafke Yan Najeriya Dake Hawa Twitter

Ekpo ya zargi gwamna Udom da rashin cika alƙawari

A wani ɓangaren rubutun da Ekpo yayi, ya zargi gwamnan jihar Akwa Ibom, Udom, da rashin cika alƙawarin da ya ɗauka a 2017 na bada kyauta ga wasu ɗalibai da suka kammala karatu a jami'ar a wancan lokaci.

Yace: "Shekara 2 da kwana 166 sun wuce amma har yanzun babu wanda yaji saƙon ko sisi. Har waɗanda suka kammala karatu da sakamako mafi kyau ba'a kula su ba sai lokacin da suka je ofishin sa."

A wani labarin kuma Duk Masu Ɗaukar Makami Su Yaƙi Najeriya Zasu Ɗanɗana Kuɗarsu, Shugaba Buhari

Shugaba Buhari ya ƙara jaddada maganarsa kan cewa duk wanda ya ɗauki makami ya yaƙi Najeriya zai fuskanci hukunci.

Shugaban yace matasa na da rawar da zasu taka domin gina goben su da kuma ƙasar su, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel