Hana Amfani da Twitter: Lai Muhammed Ya Bankaɗo Wani Asirin Twitter a Gaban Yan Majalisa

Hana Amfani da Twitter: Lai Muhammed Ya Bankaɗo Wani Asirin Twitter a Gaban Yan Majalisa

  • Ministan yaɗa labarai, Alhaji Lai Muhammed, ya fara fallasa wasu ayyukan twitter a Najeriya
  • Ministan yace twitter ya tara kuɗi ga masu zanga-zangar #EndSARS kafin daga baya a karkatar da kuɗin
  • Yanzun haka ministan na amsa tambayoyi a gaban yan majalisar kan matakin hana hawa twitter

Ministan yaɗa labarai da al'adu, Alhaji Lai Muhammed, ya bayyana cewa kamfanin twitter ya taka rawar bayan fage akan babbar zanga-zangar #EndSARS da aka yi shekarar da ta gabata, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Da Duminsa: Kotun ECOWAS Ta Dakatar da Gwamnatin Buhari Daga Cafke Yan Najeriya Dake Hawa Twitter

Ministan ya faɗi haka ne a wurin binciken dokar hana twitter da kwamitocin majalisar wakilai da suka haɗa da, kwamitin labarai, ICT da shari'a ke gudanarwa.

Ministan yaɗa labarai, Lai Muhammed
Hana Amfani da Twitter: Lai Muhammed Ya Bankaɗo Wani Asirin Twitter a Gaban Yan Majalisa Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Mr. Muhammed yace: "Kamfanin twitter ya haɗa wa masu zanga-zangar #EndSARS kuɗi, kafin daga bisani a karkatar da su ta wata hanyar."

KARANTA ANAN: Duk Masu Ɗaukar Makami Su Yaƙi Najeriya Zasu Ɗanɗana Kuɗarsu, Shugaba Buhari

Yanzu haka ministan na amsa tambayoyi a gaban yan majalisa

A yanzun haka ministan na gaban yan majalisar wakilai yana amsa wasu tambayoyi kan matakin gwamnati na hana amfani da twitter.

Yan majalisar na zargin cewa FG ta ɗauki matakin hana amfani da twitter a Najeriya ne saboda ya goge rubutun shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari.

A wani labarin kuma Shugaba Buhari Ya Amince da Gina Sabbin Jami'o'i 5 a Faɗin Najeriya

Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya amince da gina jami'o'i guda biyar a faɗin Najeriya, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Sakataren ma'aikatar ilimi ta ƙasa, Arch Sonny Echono, shine ya bayyana haka a babban birnin tarayya Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel