Da dumi-dumi: An kashe dan bindiga yana yunkurin sace wani dan kasar waje a Kaduna

Da dumi-dumi: An kashe dan bindiga yana yunkurin sace wani dan kasar waje a Kaduna

  • Dan bindiga ya hadu da ajalinsa yayin da suka yi kokarin yin garkuwa da wani dan kasar Indiya a unguwar Dankande, da ke Karamar Hukumar Igabi, Jihar Kaduna
  • Jami’an tsaro sun fatattaki ’yan bindigar yayin da suka yi kwanton-bauna da nufin yin garkuwa da bakon
  • An samo bindiga kirar AK47 guda hudu dauke da albarusai 120 da kuma wayar hannu

Rundunar ‘yan sanda a Kaduna ta tabbatar da yunkurin yin garkuwa da wani dan kasar Indiya a ranar Litinin, 21 ga Yuni, a Dankande, karamar hukumar Igabi wanda ya zama rashin sa’a ga’ yan fashi da makami.

ASP Muhammad Jalige, mai magana da yawun rundunar a cikin wata sanarwa a ranar Talata, 22 ga watan Yuni, ya ce masu garkuwar sun fara kai harin ne daga kwanton baunar da suka yi wa dan kasar wajen wanda jami’ai ke yi wa rakiya, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Kungiyar NLC za ta sake komawa yajin aiki a Kaduna

Da dumi-dumi: An kashe dan bindiga yana yunkurin sace wani dan kasar waje a Kaduna
Dan bindiga ya hadu da ajalinsa yayin da yake yunkurin sace wani dan kasar waje a Kaduna Hoto: Thisday
Asali: UGC

Sai dai kuma, jami’in dan sandan ya fafata da ‘yan bindigan cike da kwarin gwiwa wanda ya yi sanadiyyar mutuwar daya daga cikinsu yayin da wasu da dama suka tsere da raunin harbin bindiga.

Jalige ya bayyana cewa bayan faruwar lamarin, tawagar bincike sun gano wasu mujallu AK47 guda hudu cike da alburusai 120 masu rai 7.62 X 39mm, wayar hannu, gami da gawar dan fashin da aka kashe.

Ya kara da cewa, an ajiye gawar dan bindigan a dakin ajiye gawarwaki yayin da ake ci gaba da bincike kan wayar domin samun cikakken bayani a kan ‘yan ta’addan, ayyukansu, da wuraren da suke.

Ya ce:

“A ranar 21 ga Yuni, 2021 da misalin karfe 9:31 na dare, jami’an tsaro da ke rakiyar wani bako zuwa Plan Farm Phase a unguwar Dankande, a Karamar Hukumar Igabi sun yi arba da ’yan bindiga.
“Sun yi musayar wuta da su na wani lokaci amma jami’an sun fatattake su tare da tseratar da dan kasar Indiyar ba tare da wani abu ya same shi ba; A halin yanzu, ’yan bindigar sun gudu zuwa cikin daji tare da raunin harbin bindiga.
“Hadin gwiwar ’yan sanda da sojoji da ke binciken yankin a ranar 22 ga Yuni, 2021 sun gano gawar daya daga cikin ’yan bindigar, bindiga kirar AK47 guda hudu dauke da albarusai 120 da kuma wayar hannu.”

Jaridar Aminiya ta kuma ruwaito cewa Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kaduna, CP UM Muri, ya yaba namijin kokarin da suka yi na dakile harin ’yan bindigar.

KU KARANTA KUMA: Sheikh Gumi ya faɗawa gwamnatin tarayya abin da za ta yi don hana satar ɗalibai a makarantu

Sojoji sun damke wani da ake zargin ‘dan fashi ne da ke tserewa zuwa jihar Oyo da kayan sojoji da layoyi

A gefe guda, Sojoji sun kama wani da ake zargin dan fashi da makami ne a cikin motar da ya tashi daga Zuru a Kebbi zuwa Ibadan, babban birnin jihar Oyo.

Onyema Nwachukwu, mai magana da yawun rundunar ya bayyana a cikin wata sanarwa a Facebook, cewa an kama wanda ake zargin ne a kan hanyar Mokwa-Jebba a yayin da suke gudanar da bincike.

Ya ce sojojin da ke sa ido sun hangi wani a cikin motar, wanda ya ce shi Sajan Aminu Sule ne.

Asali: Legit.ng

Online view pixel