Sojoji sun damke wani da ake zargin ‘dan fashi ne da ke tserewa zuwa jihar Oyo da kayan sojoji da layoyi

Sojoji sun damke wani da ake zargin ‘dan fashi ne da ke tserewa zuwa jihar Oyo da kayan sojoji da layoyi

  • Rundunar Sojin Najeriya ta bayyana yadda sojoji suka kama wani dan fashi da ya badda kammani a matsayin matafiyi
  • Sojojin da suka yi wa wanda ake zargin tambayoyi sun karyata ikirarin da ya yi cewa kakin sojan da aka samu a hannunsa na dan uwansa ne
  • Sojoji sun tsaurara kai hare-hare kan 'yan ta'addan da ke addabar al'ummomin yankin arewacin kasar

Sojoji sun kama wani da ake zargin dan fashi da makami ne a cikin motar da ya tashi daga Zuru a Kebbi zuwa Ibadan, babban birnin jihar Oyo.

Onyema Nwachukwu, mai magana da yawun rundunar ya bayyana a cikin wata sanarwa a Facebook, cewa an kama wanda ake zargin ne a kan hanyar Mokwa-Jebba a yayin da suke gudanar da bincike.

KU KARANTA KUMA: Jam’iyyar PDP ta yi babban rashi na dan majalisarta a Nasarawa, ya sauya sheka zuwa APC

Sojoji sun damke wani da ake zargin ‘dan fashi ne da ke tserewa zuwa jihar Oyo da kayan sojoji da layoyi
Wanda ake zargin yana amsa tambayoyi Hoto: HQ Nigerian Army
Asali: Facebook

Yadda sojoji suka gano wanda ake zargin

Ya ce sojojin da ke sa ido sun hangi wani a cikin motar, wanda ya ce shi Sajan Aminu Sule ne.

Mai magana da yawun ya bayyana cewa an gano wanda ake zargin yana rike da kayan sojoji, takalmin soja, wuka, da wani abu da ake zargin laya ne.

Wanda ake zargin ya yi fallasa ga sojoji

Nwachukwu ya ce a ci gaba da bincike, wanda ake zargin ya furta cewa yana a hanyarsa ta zuwa Ogbomosho a cikin jihar Oyo, sannan ya kara da cewa rigar da takalmin na dan uwansa ne wanda yake soja.

KU KARANTA KUMA: Biloniya kike aure: An yi cece-kuce yayin da Zahra Buhari ta ce aure na nufin soyayya mara iyaka a gare ta

Sai dai, mai magana da yawun rundunar ya bayyana cewa an gano wanda ake zargin yana guduwa ne daga ayyukan soji da ke gudana a jihar Neja zuwa mafaka.

Jaridar The Cable ta ruwaito cewa sojojin sun bukaci jama'a, musamman a jihar Neja, da su kai rahoton duk wani yunkuri na 'yan fashi da ke gudu ga hukumomin tsaro.

Sojojin sun tabbatarwa ‘yan kasa masu bin doka da tsaron rayuka da dukiyoyinsu.

Sheikh Gumi ya faɗawa gwamnatin tarayya abin da za ta yi don hana satar ɗalibai a makarantu

A gefe guda, Sheikh Ahmad Gumi, fitaccen malamin addinin musulunci ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta yi sulhu da yan bindiga idan har tana son tabbatar da tsaro a makarantu, The Cable ta ruwaito.

Tun watan Disambar 2020, yan bindiga sun sace dalibai a kalla so shida a makarantu a yankunan arewa maso yamma da tsakiya inda suka sace a kalla dalibai da malamai 700.

Na baya-bayan ya afku a ranar Alhamis yayin da yan bindigan suka kai hari makarantar sakandare na gwamnatin tarayya da ke Birnin-Yauri, jihar Kebbi inda suka sace dalibai da malamai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng