Yanzu Yanzu: Kungiyar NLC za ta sake komawa yajin aiki a Kaduna

Yanzu Yanzu: Kungiyar NLC za ta sake komawa yajin aiki a Kaduna

  • Kungiyar kwadago ta kasa (NLC) ta yi barazanar komawa yajin aiki a jihar Kaduna
  • Shugaban NLC, Kwamared Ayuba Wabba ya zargi gwamna Nasir El-Rufai da kin mutunta yarjejeniyar fahimtar juna da gwamnatin tarayya ta kulla tsakaninsu
  • Ya umurci mambobinta na jihar da kungiyoyin kwadago da su tattara kan su don daukar matakin

Kungiyar kwadago ta Najeriya (NLC) ta ce za ta ci gaba da yajin aikinta na dakatar da masana'antu a jihar Kaduna.

Kungiyar ta umurci mambobinta na jihar da kungiyoyin kwadago da su tattara kan su don daukar matakin, jaridar The Nation ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Kotun Najeriya ta yanke wa wani dan bautar kasa zaman gidan yari, ta ba da dalilin hukuncin

Yanzu Yanzu: Kungiyar NLC za ta sake komawa yajin aiki a Kaduna
Kungiyar NLC na barazanar komawa yajin aiki a Kaduna Hoto: Lawcare Nigeria
Asali: UGC

Shugaban NLC, Kwamared Ayuba Wabba ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai bayan taron gaggawa na Majalisar Zartarwa na kasa da aka gudanar a ranar Talata a Abuja.

Wabba ya zargi gwamnan jihar, Nasir El-Rufai da kin mutunta yarjejeniyar fahimtar juna da gwamnatin tarayya ta kulla tsakanin NLC da gwamnatin jihar, Daily Nigerian ta ruwaito.

Ya ce kuniyar, bayan gajiyar da dukkan hanyoyi, ciki har da rubuta wasiku zuwa ga Shugaba Muhammadu Buhari da Ministan kwadago da samar da ayyuka, Chris Ngige, Kungiyar ta yanke shawarar sake komawa yajin aikin.

KU KARANTA KUMA: Tsohon tauraron Manchester United ya ziyarci gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello

FG ta yi sulhu tsakanin Kwadago da El-Rufa'i, an yi yarjejeniya

A baya mun ji cewa Gwamnatin jihar Kaduna da kungiyar kwadagon Najeriya NLC sun yi yarjejeniya kan shirin sallamar ma'aikata kimanin 7000 da gwamnatin El-Rufa'i ke shirin yi.

Tun ranar Litnin NLC ta fara zanga-zanga da yajin aiki kan abinda gwamnatin jihar tayi.

Gwamnatin tarayya a ranar Alhamis ta shirya zaman sulhu tsakanin bangarorin biyu a Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel