Sheikh Gumi ya faɗawa gwamnatin tarayya abin da za ta yi don hana satar ɗalibai a makarantu

Sheikh Gumi ya faɗawa gwamnatin tarayya abin da za ta yi don hana satar ɗalibai a makarantu

  • Babban malami Sheik Ahmad Gumi ya shawarci gwamnatin tarayya ta tuntubi yan bindiga don yin sulhu
  • Malamin ya bada wannan shawarar ne bayan yan bindiga sun sake sace dalibai da malamai a jihar Kebbi a baya-bayan nan
  • Sheikh Gumi ya kuma ce ruwan bama-bamai da sojoji ke yi wa yan bindigan zai kara janyo tabarbarewar lamura ne

Sheikh Ahmad Gumi, fitaccen malamin addinin musulunci ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta yi sulhu da yan bindiga idan har tana son tabbatar da tsaro a makarantu, The Cable ta ruwaito.

Tun watan Disambar 2020, yan bindiga sun sace dalibai a kalla so shida a makarantu a yankunan arewa maso yamma da tsakiya inda suka sace a kalla dalibai da malamai 700.

Sheikh Ahmad Gumi
Babban malamin addinin musulunci, Sheikh Ahmad Gumi. Hoto: The Cable
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Masu zanga-zangar 'Buhari Must Go' sun banka wuta a hanyar zuwa filin tashin jirage na Abuja

Na baya-bayan ya afku a ranar Alhamis yayin da yan bindigan suka kai hari makarantar sakandare na gwamnatin tarayya da ke Birnin-Yauri, jihar Kebbi inda suka sace dalibai da malamai.

Satar daliban ya janyo an dakatar da makarantun kwana an kuma tura jami'an tsaro makarantu a wasu jihohi kamar yadda Within Nigeria ta ruwaito.

Shawarar da Gumi ya bawa gwamnatin tarayya

A yayin hirar da The Punch ta yi da Gumi, ya ce hare-hare ta sama da sojoji ke kaiwa yan bindigan ba zai magance matsalar ba domin su kansu yan bindigan 'fitina ce ta saka su abin da suke yi'.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun bi basarake gidansa sun bindige shi har lahira a Kaduna

"Idan ana son tsare makarantu, mai zai hana a tattauna da yan bindigan. A tattauna da su; ba su da yawa. Za ka iya kirga su da hannun ka. Makarantu nawa za ka tsare? Ba zai yiwu ba. A dukkan arewa maso yamma, yan bindigan ba za su dara 100,000 ba. Wannan kaman digon ruwa ne a teku," in ji shi.
"Wadanda ke da makamai kenan; domin ba dukkansu ke da makamai ba. Kashi tamanin cikin dari na wadanda ke da makamai suna amfani da su ne don tsare shanunsu daga barayin shanu.
"Suma cikin fitina suke. Hare-haren sama da ake kai musu zai lalata lamarin ne domin idan ka fara kashe 'ya'yansu, ka tuna 'ya'yan mu na hannunsu."

A wani labarin daban, kun ji cewa daya daga cikin daliban da yan bindiga suka sace yayin harin da suka kai makarantar sakandare na gwamnatin tarayya da ke Birnin-Yauri a jihar Kebbi ya riga mu gidan gaskiya.

The Cable ta ruwaito cewa Abubakar Abdulkadir, mataimakin kwamandan rundunar hadin gwiwa a arewa maso yamma ne ya sanarwa manema labarai hakan a ranar Juma'a.

Kawo yanzu ba a tantance adadin daliban da yan bindigan suka sace ba yayin harin da suka kai a ranar Alhamis. Sai dai, wasu kafafen watsa labarai a Nigeria sun bayyana cewa dalibai 30 ne aka sace.

Asali: Legit.ng

Online view pixel