Kasar Isra'ila ta tsorata bayan mai tsattauran ra'ayi a kasar Iran ya lashe zabe

Kasar Isra'ila ta tsorata bayan mai tsattauran ra'ayi a kasar Iran ya lashe zabe

  • Isra'ila ta bayyana tsoronta bayan da kasar Iran ta yi sabon shugaban kasa a jiya Asabar
  • Rahotanni daga kasar Iran sun bayyana cewa, dan ra'ayin rikau ya lashe zaben kasar Iran
  • Hakazalika, kasar Isra'ila ta bayyana matakin da ya kamata sauran kasashen duniya su dauka

Rahoton da Legit.ng Hausa ta nakalto daga BBC ya bayyana cewa, Isra’ila ta shiga damuwa kan zaben Ebrahim Raisi a matsayin sabon shugaban kasar Iran.

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Isra’ila, Lior Haiat, ya ce Mista Raisi shi ne shugaban kasar Iran mafi tsaurin ra’ayi da aka taba yi a tarihi.

Ya yi gargadin cewa shugaban zai ci gaba da inganta ayyukan nukiliyar kasar Iran.

KU KARANTA: Ba zai yiwa ba: Shugaba Buhari ya ce ba ga kowane dan siyasa zai mika mulki ba

Kasar Isra'ila ta tsorata bayan mai tsattauran ra'ayi a kasar Iran ya lashe zabe
Tutocin kasashen Isra'ila da Iran a hade wuri daya | Hoto: orfonline.org
Asali: UGC

Sannan ya yi kira ga kasashen duniya su bayyana damuwa game da zabensa a matsayin shugaban Jamhuriyyar Musulunci ta kasar Iran.

An ayyana Raisi mai ra’ayin rikau a matsayin wanda ya lashe zaben Shugaban Kasar Iran

An ayyana cewa, Iran Ebrahim Raisi ya lashe zaben shugaban kasar inda zai zama shugaban kasar na takwas, kamar yadda ma’aikatar harkokin wajen kasar ta sanar.

Ma’aikatar wajen a ranar Asabar ta tabbatar da Raisi ya samu 61.95% na kuri’un da aka kada a zaben ranar Juma’ah inda aka samu masu jefa kuri’a 48.8% wanda shi ne mafi karanci tun bayan juyin juya halin shekarar 1979, rahoton Aljazeera.

Mista Raisi mai shekara 60, shi ne akalin alkalan Iran wanda ke da tsattsauran ra'ayi. Tuni Amurka ta saka masa takunkumi sannan kuma ana alakanta shi da hukunce-hukuncen da aka yanke wa 'yan adawar siyasa.

KU KARANTA: Firaministan India Ya Aikewa Buhari wasikar shawari kan lafiyar motsa jiki

A wani labarin, Jakadan Koriya ta Arewa a Najeriya Chi Tun Chon Hu, ya ce gwamnatinsu ta ba da fifiko wajen bunkasa alakar kasashen biyu, BBC ta ruwaito.

Ya bayyana hakan ne a ranar Talata a Abuja lokacin da ya ziyarci Shugaban Jam’iyyar APC na kasa.

Ya ce ya lura cewa Najeriya da Koriya ta Arewa sun yi tarayya a abu daya, inda ya ce rajistar jam’iyya da jam’iyya mai mulki a kasar ta APC ta yi a kwanan nan babbar nasara ce.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.