Yadda 'Yan Bindiga Suka Yi Amfani da Motar Mahaifin Dalibi Wajen Sace Daliban Kebbi
- Rahoto ya bayyana cewa, 'yan bindigan da suka sace daliban Yauri na jihar sun yi awon gaba da daliban a motar mahaifin dalibi
- Rahoton ya ce, mahaifin ya zo daukar dansa ne, sai kawai kwasam 'yan bindigan suka afkawa makarantar kuma suka gudu da motar
- Rahoton ya shaida cewa, an yi musayar wuta tsakanin 'yan sanda da 'yan bindigan kafin a sace daliban
Rahotanni da Legit.ng Hausa ta samo sun bayyana cewa, 'yan bindigan da suka sace dalibai a jihar Kebbi sun yi amfani da motar wani mahaifin dalibi ne wajen sace daliban.
Idan baku manta ba, wasu mahara sun kai hari kwalejin gwamnatin tarayya dake garin Yauri a jihar Kebbi a ranar Alhamis kuma sun yi awon gaba da dalibai da ma’aikata, jaridar Guardian ta ruwaito.
Wani malami da bai so a ambaci sunansa ba ya shaida wa Daily Trust cewa kafin harin, sun samu labarin wani shiri na mamaye garin na Birnin Yauri.
KU KARANTA: Bawa Ya Bayyana Yadda EFCC Zata Bankado Wadanda Ke Hana Najeriya Ci Gaba
Ya ce don hana kai hari kan makarantar, an tura rundunar 'yan sanda a makon da ya gabata.
Malamin ya ce lokacin da 'yan bindigan suka zo, sai jami'an tsaro suka yi musayar wuta da su amma suka fi karfinsu.
Ya ce bayan sace daliban, 'yan bindigan sun yi amfani da motar bas mallakar mahaifin wani dalibi wanda ya zo makarantar don daukar dansa wanda zai rubuta jarrabawar JAMB a ranar Asabar, don kwashe mutanen.
KU KARANTA: Baba Oyoyo: Muhimman Jawabai 11 da Shugaba Buhari Ya Yi a Ziyararsa Ta Borno
Dan Majalisa Ya Tabbatar da Sace Daliban Yauri Na Jihar Kebbi
A wani labarin, Dan majalisar da ke wakiltar mazabar Ngaski/Shanga/Yauri ta Tarayya ta Jihar Kebbi a Majalisar Wakilai, Yusuf Tanko Sununu, ya tabbatar da sace dalibai da malaman Kwalejin Gwamnatin Tarayya da ke Birnin Yauri dake Jihar Kebbi, Daily Trust ta ruwaito.
Sununu, wanda ya yi jawabi ga manema labarai a Majalisar Tarayya, ya ce har yanzu ba a gano adadin dalibai da malaman da aka sace ba.
A cewarsa: “Sun sami damar shiga ne bayan artabu mai karfi da suka yi da 'yan sanda wadanda ke gadin Kwalejin Gwamnatin Tarayya da ke Birnin Yauri. Sun fasa hanya zuwa makarantar.
“Sun yi nasarar yin garkuwa da wasu malamai da kuma daliban da ba a san adadin su ba. Wasu daga cikin daliban da kuma jami'an tsaron a yanzu haka suna karbar kulawa a babban asibitin Yauri sakamakon raunukan da suka samu daga bindiga."
Asali: Legit.ng