Barcelona Ta Tabbatar da Ɗaukar Fitaccen Ɗan Wasan Ƙungiyar Lyon
- Ƙungiyar Barcelona ta tabbatar da ɗaukar fitaccen ɗan wasan ƙungiyar Lyon, Memphis Depay
- Barcelona ta bayyana haka ne a wani rubutu da ta sanya a shafin ta na yanar gizo, tace ɗan wasan zai sanya hannu a yarjejeniyar shekara 2
- Depay zai yi aiki a karo na biyu tare da mai horar wa, Ronald Koeman, kuma shine ɗan wasa na 4 da Barca da ɗauka
Ƙungiyar kwallon ƙafa ta FC Barcelona ta tabbatar da cewa ta cimma matsaya na ɗaukar fitaccen ɗan wasan Lyon, Memphis Depay, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.
Ƙungiyar ta bayyana cewa ta dai-daita da ɗan wasan kuma zai sa hannu kan yarjejeniyar buga wasa na tsawon shekara biyu.
KARANTA ANAN: Shugaba Buhari Ya Buƙaci Kamfanin MTN Ya Rage Farashin 'Data' Ga Yan Najeriya
Depay zai koma ƙungiyar Barcelona da taka leda da zarar yarjejeniyarsa da Lyon ta ƙare a ƙarshen watan Yuni.
Barcelona ta rubuta a shafinta na yanar gizo cewa:
"Barcelona da Depay sun cimma matsaya cewa ɗan wasan zai dawo ƙungiyar da buga wasa da zarar yarjejeniyar da Olympique Lyonnais ta ƙare."
"Dan wasan zai sanya hannu a akan yarjejeniya zama na tsawon shakaru biyu."
Depay zai haɗu da mai horad da Barcelon, Ronald Koeman, wanda suka taɓa aiki tare lokacin da ya horad da tawagar yan wasan ƙasar Holland.
KARANTA ANAN: PDP Ta Ragargaji APC a Zaɓen Cike Gurbin da Aka Gudanar a Jihar Kaduna
Memphis Depay ya zama ɗan wasa na 4 da Barcelona ta ɗauka
Rahoton Daily trust ya bayyana cewa, kafin amincewa da ɗaukar Depay, Barcelona ta dakko ɗan wasan gaba mai zura ƙwallo, Kun Aguero, da mai tsaron baya, Eric Garcia daga Manchester City, bayan yarjejeniyar su ta ƙare.
Mai tsaron baya, Emerson Royal, shine ɗan wasa na uku da ya koma Barcelona bayan shafe shekaru biyu a matsayin aro a ƙungiyar Real Betis.
A wani labarin kuma Mu Haɗu a Filin Yaƙi, Gwamna Yayi Alƙawarin Shiga Daji Domin Yaƙi da Yan Bindiga
Gwamna Atiku Bagudu na jihar Kebbi, yayi alƙawarin shiga cikin mafarauta domin bin sawun yan bindigan da duka sace ɗaliban FGC Birnin Yauri.
Bagudu yace addini ya amince a sadaukar da rayuwa domin kare martaba, dukiya da imani.
Asali: Legit.ng