Tsoffin gwamnoni 6 a Najeriya dake fadi a ji har yanzu a siyasar jihohinsu

Tsoffin gwamnoni 6 a Najeriya dake fadi a ji har yanzu a siyasar jihohinsu

  • Wasu tsoffin gwamnoni a Najeriya suna da matukar karfin iko da rinjaye a jihohinsu kamar su ke mulkin a halin yanzu
  • Wannan ya biyo bayan aikinsu tukuru, tabbatar da siyasa mai karfi da kuma rainon kananan 'yan siyasa a lokacin mulkinsu
  • Jimillar wadannan 'yan siyasa idan aka duba su za a ga suna da magoya bayan, masoya da 'yan ga-ni-kashe-ni a jihohinsu

Akwai 'yan siyasa da kuma iyayen gida wadanda suke da wani irin karfin iko a jihohinsu na juya akalar siyasar jihar tun suna mulki har da yanzu da suka sauka, komai kuwa zafin da siyasar jihar ta dauka.

A Najeriya, wadannan iyayen gidan a siyasa suna da yawa kuma har yanzu ana mutunta su, suna da karfin iko tare da magoya baya masu tarin yawa ko bayan sun bar kujerunsu.

Kara karanta wannan

Ooni Na Ife Ya Sake Angwancewa Da Kyakkyawar Budurwa Karo Na 3 Cikin Makonni

Wadannan kwararrun a siyasa sun kiyaye yadda za a dinga damawa dasu a siyasar Najeriya tun bayan dawowar mulkin damokaradiyya a Najeriya a 1999.

KU KARANTA: Bidiyon Ahmed Musa kusa da tsadaddun motocinsa a gidansa na Kano ya kayatar

Tsoffin gwamnoni 6 a Najeriya dake fadi a ji har yanzu a jihohinsu
Kwankwaso da Lamido na daga cikin gwamonin da ke fadi a ji a jihohinsu ko bayan sun kammala mulkinsu. Hoto daga @KwankwasoRM
Asali: Twitter

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Legit.ng ta tattaro muku jerin tsoffin gwamnoni 6 a Najeriya masu juya siyasar jiharsu ko bayan saukarsu mulki.

1. Asiwaju Bola Ahmed Tinubu

Tinubu shine babban misali a irin wadannan 'yan siyasan. Tsohon gwamnan jihar Legas din shi ke jan gaban siyasar jiharsa da ta yankin kudu maso yamma.

Tinubu ya tabbatar da hawa mulkin gwamnoni 3 tun bayan da ya bar kujerar a 2007 kuma lokacin da daya daga cikinsu yayi kokarin bijire masa, Jagaban Borgu ya saka yaransu sun saita masa hanya.

2. Chief James Onanefe Ibori

Ibori ba dan siyasa bane kamar kowanne iri. Akwai wuya a samu mutum a siyasa wanda zai iya fito na fito da shi a jihar Delta. Yayin da Tinubu ke da 'yan tawaye, Ibori bashi da wata matsala tun 1999.

Kara karanta wannan

Cikakken Jawabin da 'Dan takaran APC, Bola Tinubu ya yi Daga Shigowa Najeriya

3. Emeka Ihedioha

Kusan watanni 8 yayi a kujerar gwamnan jihar, amma Ihedioha ya zama babban dan siyasa a Imo. A ziyarar karshe da ya kai jihar Imo, tun daga filin jirgi magoya bayansa suka dinga bin sa har gidansa.

Tsohon dan majalisar tarayyan ya dandana zakin siyasar jiharsa da ta tarayya amma hakan bai saka masa girman kai ba.

KU KARANTA: Hotunan cikin katafaren gidajen Mark Zuckerberg masu darajar N131b

4. Bukola Saraki

'Yan siyasa irinsu Oloye ba kasafai ake samun irinsu ba. Mutum ne da ya gaji mahaifinsa kuma ya daga sunan gidansu.

A shekaru 57 da yake a duniya, ya zama hadimin shugaban kasa, gwamna sau biyu, shugaban zauren gwamnoni, shugaban kwamitin muhalli a majalisar dattawa kuma shugaban majalisar dattawa.

5. Rabiu Kwankwaso

Babu dan siyasa mai karfin iko da magoya baya a arewa kamar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso. Ana danganta yanayin siyasarsa da ta Malam Aminu Kano.

Kara karanta wannan

Tuna baya: Akwai kalaman da Peter Obi ya yi a baya dake nuna yana goyon bayan IPOB

A duk inda ya shiga, ruwan jajayen huluna ake gani. Babu shakka halayyarsa ta gina kananan 'yan siyasa da tallafawa jama'a ne yasa yake da wadannan mabiyan.

6. Sule Lamido

Dan siyasan mai shekaru 72, Sule Lamido yana daga cikin 'yan siyasan dake fadi a ji a jiharsa.

Baya iya jurewa shirme, Lamido ya samu sunansa ne saboda yanayin ayyukansa da salon siyasarsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel