Hotunan cikin katafaren gidajen Mark Zuckerberg masu darajar N131b

Hotunan cikin katafaren gidajen Mark Zuckerberg masu darajar N131b

  • Mamallakin Facebook, Mark Zuckerberg, yana matukar kaunar harkar gidaje da mallakarsu, hakan yasa yake da gidaje a birane
  • Mutum na biyar da yafi kowa arziki a duniya yana alfahari da kadarorin da yake dasu da suka kai N131 biliyan da sauran manyan gidajensa
  • Gidan da yake zama tare da matarsa da 'ya'yansa na da girman kafa 5,617, dakunan bacci 5 da kuma sauran abubuwan kayatarwa

Mamallakin Facebook, Mark Zuckerberg yana daya daga cikin jama'a masu son tara kadarori.

Duk da 'ya'yansa biyu kacal masu shekaru 3 da 5, biloniyan yana da jerin katafaren gidaje da kadarori masu yawa da ya siya da sunansa.

KU KARANTA: EFCC ta cafke wasu mutum 3 da ake zargi da yin kudin jabu

Hotunan cikin katafaren gidan Mark Zuckerberg mai darajar N131b
Hotunan cikin katafaren gidan Mark Zuckerberg mai darajar N131b. Hoto daga Nypost
Asali: UGC

KU KARANTA: Sojoji sun halaka 'yan ta'adda masu tarin yawa a kakkabar makonni 2 da suka yi a kudu

Palo Alto, California mai darajar $50 miliyan (N20.5 billion)

Katafaren gidan Palo Alto dake California yana daya daga cikin gidajen da Zuckerberg yake kauna kamar yadda NYpost ta ruwaito.

Wannan kyakyawan gidan an gano cewa dan kasuwan ya siye shi ne shekara daya kafin ya auri matarsa.

Kamar yadda Architectural Digest suka ruwaito, ya siya gidan kan kudi $7 miliyan kuma yana da dakunan bacci 15 da bandakuna sama da 16. Gidan yana da fadin taku 20,000 kuma yana da wurin wanka da sauran ababen more rayuwa.

Lake Tahoe, California mai darajar $59 miliyan (N24.1 biliyan)

Zuckerberg na kaunar California a bayyane saboda gidan da ya mallaka a Lake Tahoe. Gidan hutun an gina shi ne a kusan aka 10 kuma yana da darajar N24.1 biliyan, ya siye shi a 2018.

Gidan mai girman kafa 5,322 yana da dakunan bacci shida, bandakuna biyar, tafki mai fadin kafa 400, dakin baki da garejin mota, Permit records suka tabbatar.

A wani labari na daban, kkungiyar matasan arewa (AYA) ta ce ta shirya fito na fito da duk mai barazana ga shugaban hukumar yaki da rashawa da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, Abdulrasheed Bawa.

Wannan na zuwa ne bayan kwanaki kadan da yace yana samun barazanar mutuwa saboda manyan da ya addaba a kan rashawa.

Marasa rinjaye a majalisar wakilai a ranar Alhamis sun yi kira ga gwamnatin tarayya da kada su yi watsi da wannan barazanar, Daily Trust ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng