Bidiyon Ahmed Musa kusa da tsadaddun motocinsa a gidansa na Kano ya kayatar

Bidiyon Ahmed Musa kusa da tsadaddun motocinsa a gidansa na Kano ya kayatar

  • Kyaftin din Super Eagles Ahmed Musa a yanzu ya koma wasa da kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars
  • Tsohon zakaran kwallon kafa a Moscow din ya kasance sha kallo a kungiyar Sai Masu Gida tun bayan da ya koma gida
  • Ahmed Musa na daya daga cikin manyan 'yan wasan kwallon kafa da ya mallaki tsadaddun motoci a garejinsa

Ahmed Musa wanda shine kyaftin din kungiyar kwallon kafa ta kasa, Super Eagles ya wallafa wani gajeren bidiyonsa a garejinsa dake jihar Kano inda yake godiya ga Ubangiji kan wannan ni'ima da yayi masa.

Dan wasan kwallon kafan Kano Pillars a halin yanzu yana daya daga cikin 'yan kwallon kafa na Najeriya masu tarin dukiya kuma duk a kwallo suka sameta.

KU KARANTA: Elon Musk ya tafka asarar N397.62bn a rana 1, ya fado daga na 2 a arzikin duniya

Bidiyon Ahmed Musa kusa da tsadaddun motocinsa a gidansa na Kano ya kayatar
Bidiyon Ahmed Musa kusa da tsadaddun motocinsa a gidansa na Kano ya kayatar. Hoto daga ahmedmusa718
Asali: Instagram

KU KARANTA: Sojoji sun halaka 'yan ta'adda masu tarin yawa a kakkabar makonni 2 da suka yi a kudu

A bidiyon da tsohon dan wasan gaba na Leicester City din ya wallafa, an ga motocin alfarma uku kusa da shi yayin da yake latsa waya kuma yana tafiya.

Ahmed Musa yayi bayanin cewa yana farin ciki tare da godiya a kan duk abinda ya samu a rayuwa.

"Farinciki hali ne. Ko dai mu zauna a cikin damuwa ko kuma mu shiga farin ciki tare da juriya. Yanayin aikin duk daya ne. Ina godiya ga Ubangiji kan duk ni'imomin da yayi min."

Tun farko, Legit.ng ta ruwaito yadda Ahmed Musa tare da sauran 'yan wasan kungiyar Kano Pillars da na Akwa United suka fita filin wasa dake Ahmadu Bello a Kaduna bayan fusatattun magoya baya sun fada filin.

A wani labari na daban, kungiyar matasan arewa (AYA) ta ce ta shirya fito na fito da duk mai barazana ga shugaban hukumar yaki da rashawa da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, Abdulrasheed Bawa.

Wannan na zuwa ne bayan kwanaki kadan da yace yana samun barazanar mutuwa saboda manyan da ya addaba a kan rashawa.

Marasa rinjaye a majalisar wakilai a ranar Alhamis sun yi kira ga gwamnatin tarayya da kada su yi watsi da wannan barazanar, Daily Trust ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel