Tauraron kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles ya auri shahararriyar jarumar fina-finan Hausa

Tauraron kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles ya auri shahararriyar jarumar fina-finan Hausa

  • Shehu Abdullahi ya sake haduwa da farin ciki a rayuwarsa yayinda ya angwance da sabuwar amaryarsa Naja’atu Muhammed Suleman a wani biki mara hayaniya
  • Kyaftin din Super Eagles kuma babban aminin Abdulahi Ahmed, Musa na daga cikin wadanda suka halarci bikin bayan sallar Juma'a
  • Mai tsaron bayan na kungiyar AC Ominia ya dawo cikin tawagar kasar bayan shekaru biyu da ya kwashe ba ya cikin tawagar Gernot Rohr

Shehu Abdullahi ya angwance da sabuwar amaryarsa Naja'atu Muhammed Suleman yayinda abokin wasansa na kasa da kasa kuma babban abokins na tsawon lokaci Ahmed Musa ya taya shi murna.

Matashin mai shekaru 28 ya saka hoton sabuwar matar tasa sannan ya rubuta "Alhamdulillah" yayinda sakon taya murna ke ta shigowa daga mabiya 193,000 a shafin na Instagram.

KU KARANTA KUMA: Alhaji Ibrahim Mohammed: Ku sadu da Sarkin makafi a Ibadan wanda ke da mata 3 da yara da yawa

Tauraron kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles ya auri shahararriyar jarumar fina-finan Hausa
Tauraron kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles ya auri shahararriyar jarumar fina-finan Hausa Hoto: @abdullahishehu
Asali: Instagram

Dan wasan na Super Eagles ya kasance cike da murmushi yayin da shi ma ya sanya hotonsa tare da Musa sanye da babbar riga.

Ya ce "Alhajin Allah" sai Musa ya amsa masa "ina taya ka murna dan uwa.”

Abdulahi ya taba yin aure ga mahaifiyar 'ya'yansa Sumayya Mustapha amma sun sha wahala a baya.

KU KARANTA KUMA: Dubi jerin birane 10 mafi wahalar zama a duniya a shekarar 2021

Tauraron na AC Ominia ya lashe gasar laliga tare da kungiyar Cypriot sannan ya yanke shawarar angwancewa da sabuwar abokiyar zaman tasa wacce ta kasance tauraruwar Kannywood tun tana ‘yar shekara goma.

Sakon taya murna na mabiyansa suka aika masa

realalinuhu ya yi martani:

“Ina taya ka murna.”

yakubmohammed_ ya ce:

“Ina taya ka murna. Allah ya sanya alkhairi amen.”

ayshatulhumairah ta aika da:

“Ina taya ka murna.”

zahradeen_sani_owner ya ce:

“Ina taya ka murna.”

freshemir:

“Ina taya ka murna oga Allah yabada zaman lfy.”

ayshasarki11 ta rubuta:

“Alhmdulilah.”

A wani labarin, Ahmed Musa wanda shine kyaftin din kungiyar kwallon kafa ta kasa, Super Eagles ya wallafa wani gajeren bidiyonsa a garejinsa dake jihar Kano inda yake godiya ga Ubangiji kan wannan ni'ima da yayi masa.

Dan wasan kwallon kafan Kano Pillars a halin yanzu yana daya daga cikin 'yan kwallon kafa na Najeriya masu tarin dukiya kuma duk a kwallo suka sameta.

A bidiyon da tsohon dan wasan gaba na Leicester City din ya wallafa, an ga motocin alfarma uku kusa da shi yayin da yake latsa waya kuma yana tafiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel