Da Ɗuminsa: Wasu Fusatattun Matasa Sun Rufe Hanyar Kaduna-Abuja

Da Ɗuminsa: Wasu Fusatattun Matasa Sun Rufe Hanyar Kaduna-Abuja

  • Wasu fusatattun mutane daga ƙauyen Unguwan Magaji sun rufe hanyar Kaduna zuwa Abuja
  • Mazauna ƙauyen sun bayyana cewa yan bindiga sun hana su noma a gonakinsu, kuma suna sace su domin ƙuɗin fansa
  • Wani mazaunin ƙauyen yace yan bindigan sun shiga har gidan shugabansu sun ɗauke iyalansa

Matafiya da dama sun taru yayin da wasu fusatattun mutane suka rufe hanyar Kaduna-Abuja saboda yawaitar hare-hare a yankin, musamman kashe wata yarinya yar shekara 13 da yan bindiga suka yi.

KARANTA ANAN: Da Ɗuminsa: Sojoji Sun Kashe Yan Bindigan da Suka Sace Ɗaliban FGC a Kebbi Sama da 80

Lamarin ya faru ne a Anguwan Magaji, ƙaramar hukumar Chikun, jihar Kaduna, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Mazauna yankin sun shaida cewa yan bindiga sun kutsa cikin gidan shugaban ƙauyen, sannan suka sace iyalansa tare da wasu mutane a ƙauyen.

Fusatattun Matasa Sun Rufe Hanyar Kaduna-Abuja
Da Ɗuminsa: Wasu Fusatattun Matasa Sun Rufe Hanyar Kaduna-Abuja Hoto: thisdaylive.com
Asali: UGC

Bamu da kwanciyar hankali a gida da gonakin mu

Wani mazaunin yankin ya bayyana cewa a halin yanzun ba su da kwanciyar hankali a cikin gidan su, kamar yadda maharan suka hana su amfani da gonakinsu saboda yawan kai hari.

KARANTA ANAN: Har Yanzun Bamu Gano Adadin Ɗaliban da Aka Sace a Kebbi Ba, Rundunar Yan Sanda Ta Yi Cikakken Bayani

Yace: "Sun hana mu zuwa gonakin mu yanzun kuma sun biyo mu har gida suna sace mu domin kuɗin fansa."

"Sun kashe yarinyar yar shekara 13 tare da wani jami'in tsaro, sannan sun sace mutanen ƙauye da dama daga ciki har da iyalan shugaban ƙauyen."

Ya ƙara da cewa abinda jama'ar ƙauyen suke so kawai shine zaman lafiya ko kuma a basu dama su kare kan su.

A wani labarin kuma Ba Zan Runtsa Ba Har Sai Dukkan Yan Gudun Hijira Sun Mallaki Mahalli, Shugaba Buhari

Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, yace ba zai runtsa ba har sai dukkan yan gudun hijira sun koma gidajen su, kamar yadda the nation ta ruwaito.

Buhari yace gwamnatinsa ba zata sassauta a yaƙin da take ba har sai ta ga bayan yan ta'adda.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262