Har Yanzun Bamu Gano Adadin Ɗaliban da Aka Sace a Kebbi Ba, Rundunar Yan Sanda Ta Yi Cikakken Bayani

Har Yanzun Bamu Gano Adadin Ɗaliban da Aka Sace a Kebbi Ba, Rundunar Yan Sanda Ta Yi Cikakken Bayani

  • Hukumar yan sanda tace har yanzun ba ta gano adadin ɗaliban da yan bindiga suka sace a jihar Kebbi ba
  • Kakakin yan sandan jihar, DSP Nafi'u Abubakar, shine ya bayyana haka ranar Jumu'a a Birnin Kebbi
  • Yace ya kamata mutane su tabbatar da labari kafin su yaɗa shi tsakanin mutane

Rundunar yan sandan jihar Kebbi, ta bayyana cewa har yanzun ba ta gano adadin ɗaliban da aka sace a makarantar kwalejin gwamnatin tarayya dake Birnin Yauri, ƙaramar hukumar Ngaski, jihar Kebbi, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Ba Zan Runtsa Ba Har Sai Dukkan Yan Gudun Hijira Sun Mallaki Mahalli, Shugaba Buhari

Kakakin yan sandan jihar, DSP Nafi'u Abubakar, shine ya faɗi haka a wani jawabi da ya fitar ranar Jumu'a a Birnin Kebbi.

Ya ƙara da cewa rahoton dake yawo cewa ɗalibai 50 maharan suka sace ba gaskiya bane.

Yace: "Har yanzun hukumar yan sanda bata gano adadin ɗaliban da yan bindiga suka sace ba. Jami'ai na kan gudanar da bincike domin kuɓutar da su."

Rundunar yan sanda tace ba ta san adadin ɗaliban da aka sace ba
Har Yanzun Bamu Gano Adadin Ɗaliban da Aka Sace a Kebbi Ba, Rundunar Yan Sanda Ta Yi Cikakken Bayani Hoto: financialnigeria.com
Asali: UGC

Hukumar yan sanda ta musanta rahoton motar da akai amfani da ita

Mr. Abubakar ya ƙara da cewa: "An jawo hankalin mu kan rahoton da wasu kafafen watsa labarai ke yaɗawa cewa maharan sun yi amfani da motar yan sanda wajen sace ɗalibai 50 daga FGC."

"Maharan sun yi amfani da wata motar Hilux fara mai lambar rijista No. kBSJ 29 mallakin alƙalin babbar kotu, kuma sun yi ƙwacen motar ne a kan hanyar Birnin Yauri."

KARANTA ANAN: Zan Saka Wa Yan Najeriya Saboda Ƙaunar da suke Nuna Mun, Buhari Yayi Jawabi a Fadar Shehun Borno

Abubakar yace a ko da yaushe hukumar yan sanda a shirye take ta bayyana wa manema labarai halin da ake ciki kan lamarin.

Ya kuma roƙi al'umma da kuma yan jarida da su tabbatar da sahihancin labari kafin su yaɗa.

A wani labarin kuma Yadda Mutanen Maiduguri Suka Tarbi Shugaban Ƙasa Buhari

Mutanen Maiduguri sun tarbi shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari, cikin murna da farin ciki, kamar yadda daily trust ta ruwaito.

Yayin da jirgin Buhari ya ɗira, babu sautin dake tashi daga bakin jama'a sai na Baba Oyoyo! Baba Oyoyo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel