Ba Zan Runtsa Ba Har Sai Dukkan Yan Gudun Hijira Sun Mallaki Mahalli, Shugaba Buhari

Ba Zan Runtsa Ba Har Sai Dukkan Yan Gudun Hijira Sun Mallaki Mahalli, Shugaba Buhari

  • Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, yace ba zai runtsa ba har sai dukkan yan gudun hijira sun koma gidajen su
  • Buhari yace gwamnatinsa ba zata sassauta a yaƙin da take ba har sai ta ga bayan yan ta'adda
  • Shugaban ya kuma yaba da namijin ƙoƙarin da jami'an tsaron sa kai suke yi na taimakawa sojoji

Shugaba Buhari ya tabbatar wa mutanen yankin arewa maso gabas cewa gwamnatin ba zata dakata da yaƙar yan ta'adda ba har sai ta ga bayan su, sannan kuma dukkan yan gudun hijira sun mallaki muhallin zama, kamar yadda the nation ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Zan Saka Wa Yan Najeriya Saboda Ƙaunar da suke Nuna Mun, Buhari Yayi Jawabi a Fadar Shehun Borno

Buhari ya bada wannan tabbacin yayin ziyarar aiki da yakai jihar Borno ranar Alhamis domin duba yanayin tsaro da kuma ƙaddamar da wasu ayyuka.

Wannan na ƙunshe ne a wani jawabi da kakakin shugaban, Malam Garba Shehu, ya fitar.

Buhari ya alaƙanta nasarorin da rundunar soji ta samu kwanan nan kan yan ta'adda a Dikwa, Danbia, Goza da kyakkyawan shiri, kayan aiki da kuma ingantaccen shugabancin soji.

Buhari ya sha alwashin maida dukkan yan gudun hijira gidajensu
Ba Zan Runtsa Ba Har Sai Dukkan Yan Gudun Hijira Sun Mallaki Mahalli, Shugaba Buhari Hoto: Buhari Sallau FB fage
Asali: Facebook

Yace: "Ba zamu huta ba har sai munga miliyoyin yan gudun hijira, waɗanda rikicin Boko Haram ya raba da mahallansu, sun koma gidajen su, kuma sun sake gina wata sabuwar rayuwa mai kyau."

KARANTA ANAN: Baba Oyoyo-Baba Oyoyo: Yadda Mutanen Maiduguri Suka Tarbi Shugaban Ƙasa Buhari

Buhari ya yaba wa jami'an tsaron sa kai dake taikawa wajen yaƙi da ta'addanci

Buhari ya yaba da namijin ƙoƙarin da jami'an tsaron sa kai, JTF, Mafarauta da yan Bijilanti suke yi wajen taimakawa jami'an tsaro.

Yace: "Ba tantama, wannan nasarar da muke samu na da alaƙa da taimakon jami'an tsaron sa kai waɗanda suka haɗa da JTF, ƙungiyoyin mafarauta, da yan Bijilanti."

"Waɗannan mutanen da suka haɗa da maza da kuma mata sun sadaukar da rayuwar su wajen ganin an dawo da zaman lafiya a Najeriya."

A wani labarin kuma Tsohon Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa Ya Buƙaci INEC Ta Dakatar da Zaɓen 2023

Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa ƙarkashin jam'iyyar HDP, Chief Ambrose Owuru, ya bukaci INEC ta dakatar da zaɓen 2023, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

Owuru ya buƙaci kotu da ƙwace mulki daga hannun Buhari ta bashi, sannan a rantsar da shi cikin gaggawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel