Jihar Kano da Legas na da matukar muhimmanci ga Najeriya, Inji Asiwaju Bola Tinubu
- Jagoran APC, Bola Tinubu ya bayyana cewa ya zama wajibi manyan jihohin ƙasar nan Kano da Lagos su cigaba da kasan cewa cikin zaman lafiya
- Tsohon gwamnan jihar Lagos ɗin ya faɗi haka ne a ya yin da ya kai ziyara fadar mai martaba sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero.
- Wannan ziyara dai na ɗaya daga cikin ayyukan da Tinubu ke yi na bikin zagayowar ranar haihuwarsa, inda ya cika shekaru 69.
Jagoran jam'iyyar APC na ƙasa, Bola Tinubu yace ya zama wajibi jihar Kano da jihar Lagos su cigaba da kasancewa cikin zaman lafiya saboda yawan al'ummar su da tattalin arziƙinsu.
KARANTA ANAN: 2023: Kan Gwamonin PDP ya rabu 2 bayan shawarar da kwamitin Gwamna Bauchi ya bada
Tinubu ya bayyana haka ne ranar lahadi lokacin da yakai ziyara fadar mai martaba sarkin Kano, Aminu Ado Bayero, kamar yadda The Cable ta ruwaito.
Wannan ziyara tasa na daga cikin ayyukan da yake yi na bikin zagayowar ranar haihuwarsa, ya cika shekaru 69 a duniya.
Tsohon gwamnan jihar Lagos ya ce jihar Ƙano da takwarar ta Lagos sun yi tarayya wajen yawan al'umma, kuma suna da ƙarfin tattalin arziƙi, ya zama wajibi waɗannan jihohin su jagoranci sauran sassa na ƙasar nan wajen zaman lafiya.
Jagoran ya ƙara da cewa ya kamata jihohin biyu su cigaba da haɗa kai, biyayya, da kuma zaman lafiya a tsakanin al'ummarsu masu bambamcin yare ko ƙabila.
Domin zaman lafiyan waɗannan jihohin babban misali ne ga sauran jihohin ƙasar nan.
Tinubu ya ce akwai buƙatar Najeriya ta dawo da zaman lafiyar da aka santa da shi, duk da cewa abu ne mai wuya ta dawo da wannan martabar saboda ƙalubalen rashin tsaro da ya baibaye ta.
KARANTA ANAN: Lokaci ya yi: Mai ba Gwamna Masari shawara ya yanke jiki ya mutu ana tsakiyar biki
A jawabin jagoran APC ɗin ya ce:
"Nigeria na cikin mawuyacin hali musamman ƙalubalen rashin tsaro da take ciki da kuma sauran ƙalubale. A halin yanzu babu ta yadda za'a sami cigaba matuƙar aka rasa zaman lafiya da kwanciyar hankali a ƙasa."
"Kano ta kasance jihar da ta fi ko wacce jiha yawan al'umma a ƙasar nan, ta na cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali duk kuwa da irin matsalolin tsaro da ƙasar ke fuskanta."
"Gwamnoni na ƙoƙarin haɗa kai don samar da ƙasar Najeriya duk kuwa da banbancin ƙalbilu da muke da su, ya kamata mu jinjina musu."
A wani labarin kuma Mutane 11 sun rasa rayukansu a hatsarin motan hanyar Bauchi da Kano
Hatsarin mota a hanyar Bauchi ya yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla 10 a daren Lahadi.
Hukmar FRSC ta tabbatar da afkuwar hatsarin, ta kuma shaidawa manema labarai lamarin.
Asali: Legit.ng