Tsohon Sarkin Kano Sanusi II ya bayyana matsayarsa game da tsayawa takarar siyasa a Najeriya

Tsohon Sarkin Kano Sanusi II ya bayyana matsayarsa game da tsayawa takarar siyasa a Najeriya

  • Khalifan darikar Tijjaniyya a Najeriya, Muhammadu Sanusi II, ya bayyana ra'ayinsa a kan siyasar kasar
  • Sanusi II ya ce ko kadan bai da ra'ayin neman wani mukamin siyasa a kasar
  • Sai dai tsohon Sarkin Kanon ya ce zai ci gaba da fadakar da mutane kan irin shugabannin da ya dace a zaba

Shugaban kungiyar darikar Tijjaniyya a Najeriya, Mallam Muhammadu Sanusi II, ya bayyana cewa baya da muradin tsayawa takarar wata kujerar siyasa a kasar.

Tsohon Sarkin Kanon ya kuma jadadda cewa zai ci gaba da wayar da kan al’umma a kan irin shugabannin da ya kamata a zaba, sashin Hausa na BBC ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Sace daliban Kebbi: Mun gazawa yaranmu, Shehu Sani ya koka

Tsohon Sarkin Kano Sanusi II ya bayyana matsayarsa game da tsayawa takarar siyasa a Najeriya
Muhammadu Sanusi II ya ce zai ci gaba da wayarwa jama'a kai kan irin shugabannin da suka cancanci a zabe su Hoto: BBC
Asali: UGC

An tattaro cewa Sanusi ya fadi hakan ne a wani taron Mukaddimai da Shehunnai na darika na farko tun bayan nada shi a matsayin Khalifan kungiyar na kasa. Ya kuma bayyana cewa wannan ra’ayi nasa ba yana nufin tsunduma kai a harkar siyasa ba ne.

Ya ce:

"Idan muna da waɗanda muka aminta muka ce za su yi wa al'umma aiki za su gyara ƙasar, sai a hadu wuri guda a taimaka musu, wannan ba tsunduma a harkar siyasa ba ne, aiki ne na gyaran ƙasa da al'umma.”

Ya ci gaba da cewa rashin aikata hakan na iya jefa al’umman Najeriya cikin babban haɗari da ƙalubale.

Ya kuma ce wajibi sai an bayar da fifiko wajen samar da ilimi musamman ga kananan yara kafin a iya magance matsalolin da ƙasar ke ciki.

KU KARANTA KUMA: Hawaye sun kwaranya yayinda wasu 'yan bindiga suka yi wa Malamin UNIBEN kisan gilla

"Idan babu ilimin nan, yaran nan da muke ganinsu ba mu sa su a makaranta ba, yayan wadansu kabilu suna can suna makaranta, nan gaba wadan nan yaran sune za sukafa kamfanoni, yaranmu su zama leburorinsu."

Tsohon Sarkin Kano Sanusi Alheri Ne Ga Najeriya, Inji Shugabannin Tijjaniyya

A wani labarin, shugabannin darikar Tijjaniyya sun bayyana zaman tsohon Sarkin Kano, Mohammadu Sanusi II shugaban Tijjaniya alheri ga Najeriya, Daily Trust ta ruwaito.

Malaman da suka bayyana hakan lokacin da suka kai ziyarar ban girma gidansa na Kaduna sun kuma ce duk mabiyansu a Najeriya da Afirka suna alfahari da shi.

Wakilin shugaban darikar Tijjaniyya na duniya, Sheikh Abdul-Ahad Nyass wanda ya jinjinawa tsohon sarkin ya ce shawara ce ta bai daya da kasancewar tsohon sarki sanusi a matsayin Khalifa a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel