Tsohon Sarkin Kano Sanusi Alheri Ne Ga Najeriya, Inji Shugabannin Tijjaniyya

Tsohon Sarkin Kano Sanusi Alheri Ne Ga Najeriya, Inji Shugabannin Tijjaniyya

- Shugabannin darikar Tijjaniya sun yaba da halayen tsohon sarkin Kano Sanusi Lamido Sanusi

- Shugabannin sun ce tabbas alheri ne nada Sanusi a matsayin Khalifan darikar a kasa Najeriya

- Sarki Sanusi ya bayyana yadda ya kau karagar Kano tare da yadda aka zabe shi a matsayin Khalifa

Shugabannin darikar Tijjaniyya sun bayyana zaman tsohon Sarkin Kano, Mohammadu Sanusi II shugaban Tijjaniya alheri ga Najeriya, Daily Trust ta ruwaito.

Malaman da suka bayyana hakan lokacin da suka kai ziyarar ban girma gidansa na Kaduna sun kuma ce duk mabiyansu a Najeriya da Afirka suna alfahari da shi.

Wakilin shugaban darikar Tijjaniyya na duniya, Sheikh Abdul-Ahad Nyass wanda ya jinjinawa tsohon sarkin ya ce shawara ce ta bai daya da kasancewar tsohon sarki sanusi a matsayin Khalifa a Najeriya.

KU KARANTA: Ya Isa Haka: Saudiyya Ta Bukaci a Tuhumi Isra'ila Kan Kisan Gilla ga Falasdinawa

Tsohon Sarkin Kano Sanusi Alheri Ne Ga Najeriya, Inji Shugabannin Tijjaniyya
Tsohon Sarkin Kano Sanusi Alheri Ne Ga Najeriya, Inji Shugabannin Tijjaniyya Hoto: change.org
Asali: UGC

Ya kara da cewa shugaban darikar Tijjaniyya na duniya Sheikh Mahi Nyass yana alfahari da nasarorin da tsohon sarki ya samu a rayuwar jama'a da kuma a matsayin masarauta.

Ya bayyana babban taron da mabiyansu suka yi zuwa Kaduna don karrama Sanusi, a matsayin shaidar yadda tsohon sarkin har yanzu ya ke da karbuwa da girma a idon mutane wadanda ke da cikakken kwarin gwiwa kan halayen jagorancinsa.

Har ila yau, Sheikh Mukhtar Adhama ya bayyana imanin cewa Sanusi a matsayin Khalifan darikar Tijjaniyya zai karfafa koyo da zurfafa ilimi a tsakanin mabiyansu.

A jawabinsa, tsohon sarki Sanusi ya tuna cewa tun kafin ya hau karagar mulki a Kano, ya ziyarci manyan Shehunai na Tijjaniyya a Kaulaha ta kasar Senegal wadanda suka yi addu’a kuma suka yi hasashen cewa zai zama sarkin Kano.

Ya tuna cewa hatta shugabancin da Tijjaniyya ta daura masa a yanzu, 80% na wadanda suka amince da shi Shehunai ne da bai san su ba.

Daga karshe ya yi addu’ar samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a Najeriya tare da gargadin ‘yan kasar da su zama masu hakuri da bin doka da oda.

KU KARANTA: Yunwa Ta Kusa Zarce Boko Haram da 'Yan Bindiga Kisa a Najeriya, Jigo a PDP

A wani labarin, An ga fostoci dauke da hotunan Gwamnan jihar Borno, Babagana Umaru Zulum tare da tsohon shugaban jam'iyyar APC ta kasa, Adams Oshiomole dake yi wa al'ummar musulmi barka da zagayowar karamar sallah.

Wakilin Legit.ng Hausa ya gano hotunan a wurare da dama a birnin Gombe, a ranar karamar wanda yayi daidai da 13 ga watan Mayu, 2021.

Hotunan na nuni da alamun cewa, Oshiomole da Zulum za su tsaya takarar shugaban kasa a zabe mai zuwa na shekarar 2023 a karkashin jam'iyyar APC kamar yadda fostar ta nuna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.