Sace daliban Kebbi: Mun gazawa yaranmu, Shehu Sani ya koka

Sace daliban Kebbi: Mun gazawa yaranmu, Shehu Sani ya koka

  • Daliban makaranta a Najeriya, musamman waɗanda ke arewacin ƙasar, ba su da kwanciyar hankalin zuwa daukar darusa a yanzu
  • Shehu Sani, tsohon dan majalisar tarayya da ya wakilci Kaduna ta Tsakiya, ya ce ba haka lamarin yake ba a zamanin baya
  • Sanatan ya koka kan yadda shugabannni suka gaza kare daliban da suke son inganta rayuwarsu ta hanyar karatu

Babu mai musun cewa abin da ya faru kwanan nan a Kebbi ya haifar da martani da maganganu masu daci game da halin kaico da tsarin tsaron Najeriya ke ciki.

Shehu Sani a ranar Juma’a, 18 ga watan Yuni, ya koka kan yadda ci gaban ya nuna cewa shugabanni sun gaza wa yaran Najeriya.

KU KARANTA KUMA: Abubuwa masu ban mamaki 4 game da Naira 100 na Najeriya da ba lallai ne ku iya sani ba

Sace daliban Kebbi: Mun gazawa yaranmu, Shehu Sani ya koka
Shehu Sani ya ce a zamanin iyayensu da nasu sun yi karatu cikin kwanciyar hankali
Asali: UGC

Tsohon sanatan ya lura cewa a lokacin da yake makaranta, satar dalibai da yara gaba daya abune da ba a jinsa kuma bakon abu ne.

A shafinsa na Facebook, ya tuna cewa a zamanin iyayensa da kakanninsa sun je makaranta cikin kwanciyar hankali.

Kalamansa:

“Iyayenmu sun je makaranta cikin kwanciyar hankali. Mun je makaranta cikin kwanciyar hankali. Yaranmu da jikokinmu ba za su iya zuwa makaranta cikin kwanciyar hankali ba. Abun kunya ne kuma abin Allah-wadai ne gazawa wannan sabon zamanin."

KU KARANTA KUMA: An yiwa barayin waya bulala ashirin-ashirin a jihar Kano

A halin da ake ciki, sa’o’i kadan bayan ‘yan bindiga sun kai hari tare da yin garkuwa da dalibai da ma’aikatan Kwalejin Gwamnatin Tarayya da ke Birnin-Yauri a Birnin Kebbi, an bayyana sunayen wasu daga cikin wadanda abin ya shafa.

'Yan bindiga sun yi amfani da motar mahaifin dalibi wajen sace daliban Kebbi

Rahotanni da Legit.ng Hausa ta samo sun bayyana cewa, 'yan bindigan da suka sace dalibai a jihar Kebbi sun yi amfani da motar wani mahaifin dalibi ne wajen sace daliban.

Idan baku manta ba, wasu mahara sun kai hari kwalejin gwamnatin tarayya dake garin Yauri a jihar Kebbi a ranar Alhamis kuma sun yi awon gaba da dalibai da ma’aikata, jaridar Guardian ta ruwaito.

Wani malami da bai so a ambaci sunansa ba ya shaida wa Daily Trust cewa kafin harin, sun samu labarin wani shiri na mamaye garin na Birnin Yauri.

Asali: Legit.ng

Online view pixel