Abubuwa masu ban mamaki 4 game da Naira 100 na Najeriya da ba lallai ne ku iya sani ba

Abubuwa masu ban mamaki 4 game da Naira 100 na Najeriya da ba lallai ne ku iya sani ba

Daga cikin dukkan kudaden Najeriya, takardar kudi na Naira 100 yana da wani abu na daban game da shi. Wani abun mamaki yana dauke da fuskar wani gwarzo na kasa kuma tsohon Kwamishinan Kudi na kasar, Cif Obafemi Awolowo wanda ya kirkiro kalmar 'naira.'

Legit.ng na gabatar maku da wasu abubuwa guda 4 da mutane basu sani ba game da tsarin kudin Najeriya na Naira 100.

KU KARANTA KUMA: Da dumi-dumi: 'Yan bindiga sun sace dalibai da yawa a jihar Kebbi

Abubuwa masu ban mamaki 4 game da Naira 100 na Najeriya da ba lallai ne ku iya sani ba
Abubuwa masu ban mamaki 4 game da Naira 100 na Najeriya da ba lallai ne ku iya sani ba Hoto: Bettmann, LinkedIn/Historyville
Asali: Getty Images

1. An kirkire shi ne shekaru 13 bayan samun yanci

Takardar kudi na Naira 100 ya samu a Najeriya a watan Janairu, 1973, a cewar History Ville. Tun daga wannan lokacin, da hoton Obafemi Awolowo aka qawata kudin.

2. Yana da alamar tabo ga masu matsalar gani

An ce ana amfani da takardar kudi na Naira dari sosai saboda yana da sauƙin ganewa, har ma masu matsalar gani za su iya fitar da shi a cikin tulin kuɗin takarda.

A cewar Naiijaquest, yana da alamun tabo ga mutanen da ke da matsalar gani. Alamun sune layuka a gefen hagu da dama na gaban kudin.

Abin lura ne cewa an gabatar da wannan ne lokacin da aka kirkiri takardar kudi na N100.

3. Kudin ne na biyar a rukunin kudaden takarda a Najeriya

Kafin samar da takardar kudi na N100 kananan kudaden da ake da su sune N5, N10, N20 da N50.

A bisa tsarin zuwa gaba, shine kudi na biyar a Najeriya, Wikipedia ta tabbatar.

4. Shine kudi mafi jan hankali

Naijaquest tace dari takardar kudi na N100 shine yafi jan hankali a cikin dukka kudade.

A wani labarin, diyar mai kudin Najeriya, Aliko Dangote, Halima ta shiga kanen labarai kuma ta birge masu amfani da shafukan intanet.

Matashiyar matar wacce kan birge masoya da rashin hayaniyarta ta ba mutane da dama mamaki bayan ta fito ta yi rawa a wani taro da ta halarta.

Sabanin yadda aka saba ganinta, matashiyar ta sha rawa a filin taro yayinda take rera wakar da ke tashi na shahararriyar mawakiya, Teni.

Asali: Legit.ng

Online view pixel