An yiwa barayin waya bulala ashirin-ashirin a jihar Kano

An yiwa barayin waya bulala ashirin-ashirin a jihar Kano

  • An yanke ma wasu maza kimanin Mutum shida hukunci a wata kotu da ke Kano
  • An kamasu da laifin kwace wayoyi a ranar Bikin Dimokiradiyya tare da makamai masu lahani
  • Wannan hukuncin ya zama ishara ga duk wani wanda yake yi ko yake da niyyan aikata haka

Wata Kotun Shari’a da ke Kano, a ranar Alhamis ta ba da umarnin a bai wa wasu maza shida bulala 20 kowanne saboda satar wayoyin hannu har guda takwas.

‘Yan sanda sun tuhumi Umar Ibrahim, Mai shekaru 25, Abba Sani, Mai shekaru 23, Abubakar Yusuf, Mai shekaru 25, Ahmad Mustapha, Mai shekaru 22, Aliyu Bashir, Mai shekaru 24, da Ahmad Musa, Mai shekaru 20, da aikata laifin daukan kayan wani.

Alkalin da ke sauraran karar, Ibrahim Sarki-Yola, ya kuma yankewa masu laifin su shida wa'adin Zaman gidan kaso har na tsawon watanni shida ba tare da biyan tara ba.

"Wannan zai zama izina ga sauran masu aikata laifi wadanda ke addabar jama'a," in ji shi.

DUBA NAN: ‘Ka yi matukar burge ni’, inji Buhari bayan da ya bude ayyuka 7 na Gwamna Zulum

An yiwa barayin waya bulala ashirin-ashirin a jihar Kano
An yiwa barayin waya bulala ashirin-ashirin a jihar Kano
Asali: UGC

KU KARANTA: Amfani da karfin bindiga kadai ba zai kawo karshen barazanar tsaro ba, Jami’in Soja

Tun a farko, Lauya mai shigar da kara, Ali Kabara, Ya bayyana wa Kotun cewa wadanda aka yanke wa hukuncin sun aikata laifin ne a ranar 12 ga Yuni a cikin garin Kano.

Yace:

”A bikin ranar Dimokiradiyya, wadanda aka yankewa hukuncin sun shirya kansu tare da muggan makamai,A inda suka kai hari tare da karbar wayoyi takwas daga wasu jama’a.
"An gano wayoyi takwas din da aka sace a hannunsu."

Laifin, in ji shi, ya sabawa sashen doka na 97 da 292 na Penal Code.

An gaza kamo Ministar da ta tafka mugun sata a Najeriya

Shugaban hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon-kasa, Abdulrasheed Bawa, ya ce ana tafka sata a bangaren gidaje.

Abdulrasheed Bawa, ya na wannan bayani a ranar Larabar nan da ya bayyana a gidan talabijin na Channels TV, sabon shugaban hukumar ta EFCC ya ce kusan 90% na satar da ake yi, suna bi ne ta hanyar mallakar gidaje.

Asali: Legit.ng

Online view pixel