Zan Saka Wa Yan Najeriya Saboda Ƙaunar da suke Nuna Mun, Buhari Yayi Jawabi a Fadar Shehun Borno

Zan Saka Wa Yan Najeriya Saboda Ƙaunar da suke Nuna Mun, Buhari Yayi Jawabi a Fadar Shehun Borno

  • Shugaba Buhari ya bayyana cewa duk ƙoƙarin da gwamnatin sa ke yi a akan yan Najeriya biyan bashi ne
  • Ya kuma ƙara da cewa gwamnatinsa zata yi iya bakin ƙoƙarinta wajen inganta rayuwar yan Najeriya
  • Buhari yace kullum yana son zuwa Maiduguri saboda anan ne ya fara riƙe muƙamin siyasa

Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, yace zai yi iya bakin ƙoƙarinsa wajen inganta rayuwar yan Najeriya, amma da farko za'a tabbatar da tsaro, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

Buhari yace yan Najeriya na binsa bashi na ba shi dama da suka yi har ya zama shugaban ƙasa.

KARANTA ANAN: Baba Oyoyo-Baba Oyoyo: Yadda Mutanen Maiduguri Suka Tarbi Shugaban Ƙasa Buhari

Kakakin shugaban, Malam Garba Shehu, ya haƙaito Buhari na cewa:

"Duk ƙoƙarin da gwamnatin mu ke yi na yin aiki tuƙuru ga yan Najeriya biyan bashi ne saboda irin ƙaunar da suka nuna mana."

Buhari ya sha Alwashin kare yan Najeriya
Zan Saka Wa Yan Najeriya Saboda Ƙaunar da suke Nuna Mun, Buhari Yayi Jawabi a Fadar Shehun Borno Hoto: Buhari Sallau Fb fage
Asali: Facebook

Shugaba Buhari ya tuna inda ya fara siyasa a rayuwarsa

Da yake jawabi a fadar mai martaba shehun Borno, shugaba Buhari ya bayyana cewa ya fara riƙe muƙami ne a matsayin gwamnan Borno, lokacin mulkin soja, ƙaraƙashin janar Murtala Muhammad.

Yace: "Na fara riƙe muƙamin siyasa ne a anan Maiduguri, kuma a kullun inason zuwa wannan gari."

Buhari ya ƙara da cewa daga baya aka naɗa shi ministan man fetur a zamanin mulkin tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo, lokacin mulkin soja.

KARANTA ANAN: Tsohon Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa Ya Buƙaci INEC Ta Dakatar da Zaɓen 2023

Buhari yaba wa gwamnan Borno, Babagana Umaru Zulum

Buhari ya yaba wa gwamnan Borno, Farfesa Babagana Zulum, bisa namijin ƙoƙarin da yake yi na kawo cigaba a jihar, duk da ƙalubalen tsaro da ake fama da shi a jihar.

Yace yan kaɗan ne daga cikin shugabanni zasu iya irin yadda Zulum ke yi musamman yadda ya bada rayuwarsa domin kare al'ummar jihar da yake jagoranta.

A wani labarin kuma Yadda Zamu Fitar da Wanda Zai Gaje Ni a 2023, Gwamna Ganduje

Duk da raɗe-raɗin da ake yi kan wane ɗan takara APC zata tsayar a zaɓen gwamnan Kano na 2023. Gwamna Ganduje yayi magana kan yadda za'a fitar da magajin shi, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Ganduje yace idan ka duba abinda yafaru a baya wajen tsaida ɗan takara zakaga akwai rikitarwa a ciki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel