Yadda Zamu Fitar da Wanda Zai Gaje Ni a 2023, Gwamna Ganduje
- Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano, yayi tsokaci kan wanda zai gaji kujerarsa ta gwamna a jihar Kano
- Ganduje yace idan ka duba abinda yafaru a baya wajen tsaida ɗan takara zakaga akwai rikitarwa a ciki
- Wannan na zuwa ne bayan tsofaffin yan takarar gwamna a Kano guda 3 sun sauya sheƙa zuwa APC
Duk da raɗe-raɗin da ake yi kan wane ɗan takara APC zata tsayar a zaɓen gwamnan Kano na 2023. Gwamna Ganduje yayi magana kan yadda za'a fitar da magajin shi, kamar yadda daily trust ta ruwaito.
KARANTA ANAN: Gwamnatin Jihar Kano Ta Bayyana Dalilin da Yasa Ganduje Ya Taka Hoton Kwankwaso
Hakanan gwamnan ya kuma yi tsokaci kan yadda APC zata fitar da ɗan takarar shugaban ƙasa duk da jita-jitar da ake yaɗawa cewa za'a kai takarar wani yanki.
Yayin da yake amsa tambayoyi a taron manema labarai, Gwamna Ganduje na jihar Kano yace wakilan jam'iyyar APC ne zasu zabi wanda zai tsaya takara ƙarƙashin jam'iyya, kamar yadda vanguard ta ruwaito.
"Wakilai ne zasu zaɓi ɗan takara. Idan ka duba abunda ya faru a wancan lokacin zaka ga abun akwai rikitarwa, amma lokaci na zuwa, za'a warware matsalar cikin sauƙi." inji Ganduje.
KARANTA ANAN: Cece-Kuce Yayin da Gwamna Ganduje Yasa Ƙafa Ya Take Hoton Madugun Kwankwasiyya, Rabi'u Musa Kwankwaso
Wannan na zuwa ne kwanaki uku bayan wasu tsofaffin yan takarar gwamna 3 sun sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC a jihar.
Salihu Sagir Takai, A.A. Zaura da kuma Umar Yakubu Danhassan, sune waɗanda suka sauya sheka zuwa APC kwanan nan, kuma ina kallon zasu iya neman wannan kujera.
Bayan waɗannan akwai manyan jigogin jam'iyyar da ka iya neman takarar gwamna, kamar mataimakin gwamna, Nasiru Gawuna, da sanatan dake wakiltar Kano ta arewa, Bara'u Jibrin.
A wani labarin kuma Ka Shirya Wa Kawo Hari Jiharka, Wata Ƙungiya Tayi Wa Gwamna Barazana Saboda Hana Kiwo
Wata ƙungiya da ba'a santa ba tayi watsi da dokar hana makiyaya kiyo a fili a kudancin ƙasar nan
Ƙungiyar ta bayyana matakin da zata ɗauka matuƙar gwamnan Delta, Ifeanyi Okowa, ya cigaba da goyon bayan wannan dokar.
Asali: Legit.ng