Da dumi-dumi: APC ta tabbatar da dakatar da tsohon hadimin Buhari a Kano

Da dumi-dumi: APC ta tabbatar da dakatar da tsohon hadimin Buhari a Kano

  • Jam'iyyar APC a jihar Kano ta jadadda batun dakatar da tsohon mai taimakawa shugaban kasa Muhammadu Buhari kan harkokin yada labarai, Shaaban Ibrahim Sharada na shekara daya
  • Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa daga shugaban APC a yankin, Alhaji Sani Abubakar Maifata da sakatarensa, Kamilu Saidu Bala
  • Sun ce abun da Sharada ke aikatawa na iya haddasa hargitsi a jihar ta Kano

Jam’iyyar All Progressive Congress (APC) a Kano ta tabbatar da dakatar da Shaaban Ibrahim Sharada, tsohon hadimin Shugaban kasa Buhari.

Dakatarwar da aka yi wa Shaaban wanda zai kwashe tsawon watanni 12, ya biyo bayan zarginsa da aikata abunda ka iya haifar da durkushewar jam’iyyar jaridar The Guardian ta ruwaito

Da dumi-dumi: APC ta tabbatar da dakatar da tsohon hadimin Buhari a Kano
Shaaban Ibrahim Sharada tare da Shugaban kasa Muhammadu Buhari Hoto: Shaaban Ibrahim Sharada
Asali: Facebook

A wata sanarwa da shugaban APC a karamar hukumar ta birnin da kewaye ta Kano, Alhaji Sani Abubakar Maifata da sakatarensa, Kamilu Saidu Bala suka sanya wa hannu kuma suka rabawa manema labarai a ranar Alhamis, an tabbatar da dakatarwar, jaridar Vanguard ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Da dumi-dumi: 'Yan bindiga sun sace dalibai da yawa a jihar Kebbi

Jawabin ya ce:

“Don haka muna tabbatar da dakatar da Shaaban Ibrahim Sharada kamar yadda tun da farko yankin Sharada ta bayyana na tsawon watanni 12 saboda kai hare-haren da yake yi a fili da kuma jefawa Gwamna Ganduje da sauran Jiga-jigan Jam’iyyar da magana.
“A bisa ga karar da aka samu daga magoya bayan APC daga yankin Sharada, mun kafa kwamitin ladabtarwa na mutum bakwai kuma muka ba su kwanaki bakwai su gabatar da rahotonsu game da batun sannan mu yanke hukunci na karshe.
“Bayan bin diddigin rahotanninsu da shaidun da ke kunshe da dakatarwar da shugabannin gudanarwa suka yi, Kwamitin ya tabbatar da cewa an samu Ibrahim Sharada da dukkan tuhume-tuhumen da ake yi masa na kisan halayyar da yake yi wa Mai Girma Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje da sauran shugabannin jam’iyya a matakin unguwa, kananan hukumomi da kuma jihar.”

KU KARANTA KUMA: Ibo ne manyan masu hannun jari a Najeriya, ba za mu fice ba - In ji Iwuanyanwu

Ya ci gaba da cewa

“Zargin da ake kan Ibrahim Sharada na iya haddasa rikici da hargitsi a jihar wanda ka iya shafar kyakkyawan kudirin Gwamna Ganduje.
“Suna kuma iya zubar da martaba da kimar shugabannin jam’iyyar baya ga asarar jam’iyya da magoya baya a matakin farko.
"Saboda haka muna tabbatar da dakatar da Shaaban Ibrahim Sharada na tsawon watanni 12 wanda ba zai tsoma baki a dukkan harkokin jam'iyyar ba a dukkan matakai."

APC ta dakatar da Sharada, dan majalisa mai adawa da Ganduje

A baya mun kawo cewa jam’iyyar APC a jihar Kano ta dakatar da Hon Sha’aban Ibrahim Sharada, dan majalisar wakilai da ke wakiltan yankin karamar hukumar birni da kewaye na Kano, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

An dakatar da Sharada wanda ke sukar Gwamna Abdullahi Ganduje na tsawon shekara daya.

Jaridar Daily Nigerian ta kuma ruwaito cewa an dakatar da Sharada ne bisa zarginsa da ayyukan da suka saba jam’iyya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel