Da dumi-dumi: 'Yan bindiga sun sace dalibai da yawa a jihar Kebbi

Da dumi-dumi: 'Yan bindiga sun sace dalibai da yawa a jihar Kebbi

  • Wasu 'yan bindiga sun yi awon gaba da dalibai da dama a Kwalejin Tarayya da ke garin Yauri a jihar Kebbi
  • An tattaro cewa maharan sun kuma harbi wasu da dama daga cikin daliban a yayin da suke kokarin tserewa
  • Maharan dai sun sha karfin masu tsaron makarantar ne sannan suka kwace motoci kirar Toyota Hilux daga wurinsu inda suka zuba daliban sannan suka tafi da su

Labari da muke samu a yanzu ya nuna cewa wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da dalibai masu yawa daga Kwalejin Tarayya da ke garin Yauri a jihar Kebbi.

Sashin Hausa na BBC ta ruwaito cewa shaidar gani da ido sun ce maharan sun yi awon gaba da dalibai da dama sannan suka harbi wasu daga cikinsu.

KU KARANTA KUMA: Ibo ne manyan masu hannun jari a Najeriya, ba za mu fice ba - In ji Iwuanyanwu

Da dumi-dumi: 'Yan bindiga sun sace dalibai da yawa a jihar Kebbi
Rahoto ya kawo cewa 'yan bindiga sun sace dalibai da yawa a jihar Kebbi
Asali: Original

An tattaro cewa wani da abun ya faru a kan idonsa ya sanar da sashin labaran cewa 'yan bindigar sun ci karfin 'yan sandan da ke gadin makarantar sannan suka kwace motoci kirar Toyota Hilux daga wurinsu inda suka zuba daliban sannan suka tafi da su.

An kuma ruwaito cewa maharan wadanda suka kai wa makarantar hari a kan babura sun fito ne daga dajin Rijau da ke makwabtaka.

Har ila yau, an rahoto cewa an kai dalibai da dama asibiti domin samun kulawar likitoci sakamakon raunukan da suka ji na harbi a yayin da suke tserewa daga harin na 'yan bindiga.

Dan majalisar da ke wakiltar yankin a majalisar dokokin tarayya, Muhammad Bello Ingaski ya shaida wa sashin labaran na BBC cewa 'yan bindigar sun sace dalibai maza da mata da tsakar ranar Alhamis.

KU KARANTA KUMA: Da Dumi-Dumi: Buhari Ya Isa Borno, Ya Bukaci Sojoji Su Kara Daura Damara

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa kalla dalibai 30 da malamai uku aka sace a harin kamar yadda majiyoyin tsaro suka bayyana.

'Yan bindiga sun kashe ɗan sanda, sun sace 'yan ƙasar waje da ke aikin layin dogo na Legas zuwa Ibadan

A wani labarin, mun ji cewa an kashe wani jami'in dan sanda sannan an sace wasu yan kasar China su hudu da ke aiki a layin dogo na Legas zuwa Ibadan kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Wakilin majiyar Legit.ng ya ruwaito cewa yan bindigan sun labe ne a kan iyakar Adeaga/Alaagba wani gari da ke kan iyakar jihohin Oyo da Ogun a ranar Laraba.

Yan bindigan sanye da bakaken kaftani sun kutsa wurin da ake aikin layin dogon a kauyen Adeaga/Alaagba da ke karamar hukumar Odeda a jihar Ogun.

Asali: Legit.ng

Online view pixel