Da dumi-dumi: APC ta dakatar da Sharada, dan majalisa mai adawa da Ganduje
- Jam'iyyar APC mai mulki ta dakatar da Hon Sha’aban Ibrahim Sharada, dan majalisar wakilai da ke wakiltan yankin karamar hukumar birni da kewaye na Kano
- Kwamitin da jam'iyyar ta nada domin binciken zarge-zargen da ake masa ta same shi da laifi
- Dakatarwar zai ci gaba da aiki har tsawon shekara guda sannan ba zai shiga harkokin jam'iyyar ba a dukkan matakai
Jam’iyyar All Progressives Congress jihar Kano ta dakatar da Hon Sha’aban Ibrahim Sharada, dan majalisar wakilai da ke wakiltan yankin karamar hukumar birni da kewaye na Kano, jaridar Daily Trust ta ruwaito.
An dakatar da Sharada wanda ke sukar Gwamna Abdullahi Ganduje na tsawon shekara daya.
KU KARANTA KUMA: 2023: Ibrahim Shekarau ya bayyana daga yankin da ya kamata APC ta fitar da dan takarar Shugaban kasa
Jaridar Daily Nigerian ta kuma ruwaito cewa an dakatar da Sharada ne bisa zarginsa da ayyukan da suka saba jam’iyya.
An tattaro cewa kwamitin ladabtarwa na mutum bakwai da aka kafa domin binciken zarge-zargen da ake yi masa sun same shi da laifi.
Jam’iyyar ta kuma bayyana cewa an haramtawa Sharada shiga dukka harkokin jam’iyyar a dukkan matakai.
“An samu Hon. Sha’aban Ibrahim Sharada da aikata laifin da ake tuhumarsa da shi na kisan halayyar mai girma Gwamnan Kano da kuma shugabannin jam’iyya daban-daban daga shiyya, Karamar Hukuma da Matakin Jiha.
"Cewa ba zai tsoma baki a dukkan harkokin jam'iyyar da ayyukanta ba a dukkan matakai," kamar yadda wasikar da kwamitin ya karanta.
KU KARANTA KUMA: Da dumi-dumi: INEC ta sanya ranar gudanar da zabukan gwamnonin Ekiti da Osun
A wani labarin, tsohon kakakin majalisar wakilai, Alhaji Ghali Umar Na’Abba, ya caccaki gwamnoni a Najeriya yana mai cewa sun lalata dimokiradiyyar kasar, Daily Trust ta ruwaito.
Na’Abba, yayin da yake magana a wata hira da Sashen Hausa na BBC a ranar Talata, ya ce gwamnonin jihohi sun lalata dimokiradiyya, suna yin magudi a zabukan fidda gwani na jam’iyyunsu na siyasa don wanda suke so ya fito.
Ya kara da cewa gwamnonin sun kuma toshe damar da matasa za su iya shiga siyasa "wanda hakan babbar barazana ce ga makomar kasar."
Asali: Legit.ng